Jonathan Ya Ce Boko Haram Ta Taba Zabar Marigayi Buhari a Matsayin Wakili

Jonathan Ya Ce Boko Haram Ta Taba Zabar Marigayi Buhari a Matsayin Wakili

  • Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya ce Boko Haram ta taɓa zaɓar Muhammadu Buhari a matsayin mai sasanci da gwamnati
  • Goodluck Jonathan ya bayyana haka ne a lokacin bikin ƙaddamar da littafin tsohon hafsun tsaro, Janar Lucky Irabor, a Abuja
  • Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa matsalar Boko Haram na da sarkakiya, domin har bayan Buhari ya bar mulki rikicin bai ƙare ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya ce kungiyar Boko Haram ta taɓa zaɓar marigayi Muhammadu Buhari a matsayin wakilinta domin tattaunawa da gwamnati.

Jonathan ya ce wannan lamari ya faru ne a lokacin da gwamnatinsa ta kafa kwamitoci daban-daban don sasanci da mayakan kungiyar.

Jonathan tare da marigayi Muhammadu Buhari
Jonathan tare da marigayi Muhammadu Buhari. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Abuja, yayin bikin ƙaddamar da littafin da tsohon hafsun tsaro, Janar Lucky Irabor, ya rubuta.

Kara karanta wannan

'Rashin tsaro ba zai kare yanzu ba,' Gwamna ya fadawa 'yan Najeriya gaskiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Boko Haram ta taba zaben Buhari inji Jonathan

Jonathan ya bayyana cewa da ɗaya daga cikin kwamitocin da gwamnatinsa ta kafa, mayakan Boko Haram suka zaɓi Muhammadu Buhari a matsayin wakilinsu na tattaunawa.

Ya ce hakan ya sa ya yi tsammani cewa lokacin da Buhari ya hau mulki, zai iya amfani da wannan damar wajen tattaunawa da su har su miƙa makamansu.

A cewarsa, hakan bai faru ba, domin har yanzu rikicin Boko Haram ya ci gaba da kasancewa a Najeriya.

Jonathan ya ce wannan na nuna cewa batun Boko Haram ba abu ne mai sauƙi ba, kamar yadda wasu ke tunani.

Jonathan: 'Boko Haram na da sarkakiya'

Tsohon shugaban ƙasan ya ce Boko Haram ta fara ne tun shekarar 2009 lokacin da shi ya ke mataimakin shugaban ƙasa, kafin ya gaji marigayi Umaru Musa Yar’Adua a 2010.

Jonathan ya ce tsawon shekaru biyar yana fafutukar shawo kan rikicin amma ba a samu nasara a ƙarshe ba.

Kara karanta wannan

Jonathan: An fitar da dalilai kan karyata alakar Buhari da Boko Haram

Daily Post ta rahoto ya ce shi da kansa ya yi tsammani cewa Buhari, wanda ya gaje shi, zai kawar da Boko Haram cikin kankanin lokaci, amma har yanzu rikicin ya na nan.

Jonathan ya ce matsalar Boko Haram ta fi abin da ake iya gani a fili, kuma ba wai abu ɗaya ne ya haddasa rikicin ba.

Salon da za a yaki Boko Haram da shi

Jonathan ya yi kira da a duba batun Boko Haram da sabon salo, ba wai ta hanyar da aka saba kawai ba.

Ya yaba wa Janar Lucky Irabor kan yadda ya rubuta littafi mai ɗauke da bayanai kan rikicin, yana mai cewa irin rubuce-rubucen su ne ke taimakawa wajen fahimtar gaskiyar tarihi.

Tsohon hafsun tsaro, Janar Irabor
Tsohon hafsun tsaro, Janar Irabor. Hoto: Defence Headquaters
Source: Facebook

Ya kuma bukaci dukkan hafsoshin soja da suka yi aiki a lokacin rikicin Boko Haram da su fito da bayanai kan hakikanin manufar kungiyar.

Maganar takarar Jonathan a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa ana maganganu kan yin takarar shugaba Goodluck Jonathan a zaben 2027.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa kotu ce za ta yi hukunci kan ko zai iya tsayawa takara duk da ya sha rantsuwa sau biyu a baya.

Kara karanta wannan

Bayan kalaman Jonathan, Obasanjo ya yi magana kan rikicin Boko Haram

Wasu lauyoyi sun bayyana cewa rantsuwar da ya yi a karon farko ta maye gurbin marigayi Umaru Musa Yar'adua ce saboda haka ba za ta shafe shi ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng