Triumph: An Shawarci Abba game da Kalaman Mataimakinsa, Sagagi kan Zargin Taba Annabi
- An shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ji tsoron Allah wajen gudanar da shura kan zargin taba martabar Annabi SAW
- Mutane na nuna damuwa kan maganganun na kusa da gwamnan, musamman mataimakimsa, Aminu Abdussalam Gwarzo da Shehu Sagagi
- Hon. Aminu Sulaiman Maidoki ya bukaci gwamnan ya tabbatar da gaskiya da adalci ba tare da fifita wani bangare ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Yayin da ake ci gaba da bayyana ra'ayoyi kan zargin Malam Abubakar Lawan Triumph da taba kimar Annabin SAW, an ba gwamna shawara.
Daya daga cikin yan siyasa kuma dattijo a Kano, Hon. Aminu Sulaiman Khalid Maidoki ya shawarci Abba Kabir Yusuf ya yi taka-tsantsan.

Source: Twitter
Triumph: Shawarar da aka ba Gwamna Abba
Hakan na cikin wani bidiyo da shafin Da'awatus Sunnah ya wallafa a Facebook a yau Juma'a 3 ga watan Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan
Matasa sun yi zanga zangar tir da kalaman Gwamnan Kano na a cire kwamishinan 'yan sanda
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, Maidoki ya tsage gaskiya tare da shawaratar gwamnan ya ji tsoron Allah wurin tabbatar da adalci a lamarin.
Ya ce:
"Ka kafa wannan kwamitin shura da ka yi a wannan lokaci mai wahala, kuma ina rokon Allah ya ba ka dacewa kan haka, muna fatan zatonmu don Allah ka yi shi, a yanzu, ka fara samun cikas a wadansu abubuwa, ka yi nufin alheri amma ka fara samun wadanda suke yi maka kafar ungulu a tafiyarka.
"Ka kafa shura ka saka malamai waɗanda suka isa suka san mene ne martabar Annabi SAW, da su yi duba kan lamarin su yi wa Malam Lawan wa'azi, idan kuma a kan daidai yake a bar shi ya ci gaba."
Damuwar Maidoki game da kalaman mataimakin gwamna
Maidoki ya bayyana damuwa kan yadda wasu na jikin gwamnan suka fara sakin maganganu da ba su dace ba musamman da ya shafi matsalar da ake ciki.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta yi martani kan zargin jefa 'yan Najeriya miliyan 15 a bakin cikin talauci
"Tun kafin a je ko ina, mataimakinka ya fito ya yi azarbabi wanda bai dace ba, muna kira a gare ka idan ba da yauwanka ya yi ba, to ka taka masa birki.
"Na biyu ka taba ba Shehu Sagagi shugaban ma'aikata amma ka cire shi saboda zarge-zarge da rashin gaskiya.
"Duk da haka ka ba shi babban mukami mai girma wanda bai cancanci hakan ba, shi ne sakataren shura.
"Shi ma tun kafin a je ko ina, ya nuna kansa, Sagagi ya fitar da bayanai masu cin karo na juna."
- Hon. Maidoki

Source: Facebook
Abin da Hon. Maidoki ke bukata
Maidoki ya ce Sagagi ya fitar da maganganu guda biyu da suke magana kan dakatar da Lawan Triumph da suke da rikitarwa inda ya ke bukatar sanin wacece ta gaskiya a ciki.
Ya kara da cewa:
"Na farko ya ce shura ta ba da shawara a dakatar da Malam Lawan daga duk wani shiri da yake yi, a daya bangaren ya ce an ba da shawarar dakatar da shi tattauna batun da ake yi yanzu."
Ya ce gwamnan yana da burukan da yake son cimma wa, kuma ya sani hanyar da zai cika burinsa ba lallai da dace da ra'ayin wasu ba.
Triumph: Sheikh Ibrahim Khalil ya kawo mafita
Kun ji cewa Sheikh Ibrahim Khalil ya ce ba za a iya warware rikicin malamai da ake fama da shi a Kano ta hanyar mukabala da juna ba.
Shehin ya bukaci a koma kan tsarin Shehu Usman Dan Fodiyo wajen warware matsalolin addini da suke faruwa a Kano.
Baya ga haka, Shehin ya gargadi malamai da mabiyan Izala da Darika da su tsaya a layinsu ba tare da zargin juna da batanci ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
