"Akwai Rikitarwa," Jonathan Ya Bayyana Abin da Mutane ba Su Sani ba game da Boko Haram
- Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya ce kungiyar Boko Haram ta masa tabon da ba zai taba mantawa da shi ba
- Jonathan ya kuma bayyana cewa matsalar Boko Haram tana da matukar rikitarwa fiye da tunanin mafi yawan 'yan Najeriya
- Ya yaba wa Janar Lucky Irabor bisa littafin da ya rubuta kan Boko Haram, yana mai cewa hakan zai taimaki shugabanni
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa a wani lokacin mayakan Boko Haram sun fi sojojin Najeriya makamai.
Jonathan ya bayyana cewa rikicin kungiyar ta'addanci ta Boko Haram na da rikitarwa da rudani fiye da yadda mutane ke tsammani.

Source: Getty Images
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Shugaba Jonathan ya faɗi haka ne a Abuja a taron ƙaddmar da littafin “Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum."

Kara karanta wannan
Martanin da Sarki ya yi bayan zargin Peter Obi da rashin mutunta shi a sakon taya murna
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor (Mai ritaya) ne ya rubuta wannan littafi game da rikicin Boko Haram da ya ki ci yaki cinye wa a Najeriya.
Abin da Jonathan ya fahimta kan Boko Haram
Jonathan ya ce sabanin sauran rikice-rikicen da Najeriya ta sha fama da su kamar tsagerun Neja Delta, rikicin kabilanci da na addini, matsalar Boko Haram ta fi tsanani saboda alaƙarta da ƙungiyoyin waje, tsattsauran ra’ayi, da makamai.
“Boko Haram ta wuce yadda mutane ke tunani, a wani lokaci, sun fi sojojinmu makamai, wanda ke nuna akwai yan ƙasashen da ke da hannu a lamarin,” in ji Jonathan.
Ya ce sace ’yan matan Chibok a shekarar 2014 na daga cikin raunukan da suka fi ci masa zuciya a lokacin mulkinsa.
Tabon da Boko Haram ta yi wa Jonathan
Tsohon shugaban kasar ya kara da cewa ba ya tunanin akwai maganin da zai goge tabon da sace matan makarantar Chibok ya yi masa a zuciya har karshen rayuwarsa.
Jonathan ya kuma tuna yadda a matsayinsa na mataimakin shugaban ƙasa ya shiga sansanonin tsagerun Neja Delta ba tare da rakiya ta tsaro ba.
“A yankin Niger Delta, na shiga sansanonin ’yan tawaye. Mun sami nasarar dawo da zaman lafiya ba da karfin soja ba, mun tattauna da su, mun saurare su, sannan an tallafa masu. Wannan dabara ce ta yi aiki,” in ji shi.
Taya za a iya magance matsalar Boko Haram?
Sai dai ya ce kalubalen Boko Haram ya sha bamban da wannan, a cewarsa, dole a yi amfani da tsari da ya haɗa da matakan tsaro, mulki nagari, rage talauci, ƙarfafa matasa, da tabbatar da adalci a cikin al’umma.
A ruwayar Punch, Jonathan ya ci gaba da cewa:
"Ba zai yiwu mu dauki Boko Haram a matsayin matsalar karya doka kadai ba, tushen matsalar su ne talauci, wariya, da ruguza burikan mutane. Sai mun hada dabaru ta kowane bangare kafin dawo da zaman lafiya."

Source: Twitter
Ya yabawa Janar Irabor saboda rubuta abubuwan da ya gani, yana mai cewa littafin zai kara fahimtar da kasa game da 'yan tayar da kayar bayan tare da zama jagora ga shugabanni na gaba.
Sakon Jonathan ga 'yan Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su karaya duk da ƙalubalen da ake ciki a Najeriya.
Jonathan ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa na fatan alheri ga ‘yan Najeriya a ranar bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai.
Ya ce bikin samun 'yancin kan ya ba Najeriya damar tunani kan tafiyar da ta yi wajen gina kasa, ciki har da kalubalen da aka fuskanta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

