Martanin da Sarki Ya Yi bayan Zargin Peter Obi da Rashin Mutunta Shi a Sakon Taya Murna
- Sabon Sarkin Ibadan ya yi martani bayan maganganu da ake yi game sakon taya murna da Peter Obi ya aika masa da ya hau karaga
- Sarkin na Ibadan, Oba Rashidi Adewolu Ladoja, ya bayyana cewa bai ɗauki zancen Peter Obi da ya kira shi ɗan’uwa a matsayin raini ba
- Ladoja ya ce me zai sa ya fusata, ai Peter Obi abokinsa ne, kuma ɗan’uwansa, ya kuma ambaci karin maganar Yarbawa kan abota da sarauta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Sabon Sarkin Ibadan, Rashidi Adewolu Ladoja ya bayyana matsayarsa kan kalaman Peter Obi a sakon taya shi murna.
Basaraken ya fayyace cewa bai ji haushi ba kan maganar ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi, wanda ya kira shi “ɗan’uwa.”

Source: Facebook
Wannan bayani ya fito daga bakin Farfesa Pius Abioje, malamin addini, a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafin TikTok.

Kara karanta wannan
Magana ta fito, an ji dalilin da ya sa Atiku Abubakar ke jan kafa kan batun takara a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Olubadan: Reno Omokri ya dura kan Peter Obi
Wannan martani na Sarkin ya biyo bayan ce-ce-ku-ce da ake ta yi bayan tsohon dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi ya taya shi murna.
Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri shi ne ya caccaki Obi game da rubutunsa inda ya ce tsohon gwamnan bai mutunta basaraken ba.
A cikin wani rubutu da Obi ya yi, ta taya Rashidi Ladoja murna inda ya kira shi da 'dan uwana' wanda hakan ya jawo maganganu.
Omokri ya ce kwata-kwata Obi bai mutunta basaraken ba inda ya ce ko kusa ba zai taba kiran wani Sarki daga Arewacin Najeriya kamar haka ba.
Sai dai daga baya, Obi ya fitar da wata sanarwa da yake karin haske kan lamarin da cewa shi fa yana nufin dan uwa, a matsayin yayansa yake Sarkin ba kamar yadda aka dauka ba.

Source: Facebook
Abin da Sarkin Ibadan ya ce kan lamarin
A cikin bidiyon, Farfesa Abioje bayyana cewa sun tattauna ne da Sarki ta waya kan lamarin.
A cewar Abioje, lokacin da aka tambayi Ladoja ko yana fushi da Obi, sai ya ce:
“A’a, me zai sa in fusata da abokina da ɗan’uwana?”
Sarkin ya ƙara da kawo karin magana ta Yarbawa da ke cewa:
“Wanda bai son abokinsa ya zama Sarki, shi ma ba ya son Sarki ya kasance abokinsa.”
Amma kalaman Olubadan sun tabbatar da kyakkyawar dangantaka tsakaninsa da tsohon gwamnan Anambra.
Har ila yau, kalaman na shi sun kawo ƙarshen ce-ce-ku-ce da ake ta yi a kafafen sada zumunta wanda ya fusata wasu daga cikin al'umma.
Abin da Sarkin Ibadan ya fadawa Atiku, El-Rufai
A wani labarin, kun ji cewa sabon Sarkin Ibadan a jihar Oyo, Oba Rashidi Ladoja ya karbi bakuncin manyan 'yan siyasa a fadarsa.
Sarkin ya gana da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai bayan nada shi a sarauta.
Mai Martaba Ladoja ya ce ya daina siyasa bayan nadinsa inda ya tuna alakarsa da Atiku da sauran yan siyasa a baya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
