Hadimin Gwamna Ya Fusata, Ya Ajiye Mukami bayan Sauya Shekar Eno zuwa APC a Akwa Ibom
- Hadimin Gwamna Umo Eno, Ndianaabasi Udom, ya yi murabus daga mukaminsu na shugabancin hukumar titunan karkara ta jihar Akwa Ibom
- Udom, wanda ke cikin kwamitin rikon PDP na jihar, bai bayyana dalilin murabus dinsa ba, sai dai ana alakanta haka da rikicin siyasa
- Siyasar jihar ta fara rincabe wa tun bayan da Gwamna Umo Eno ya fice daga PDP, tare da jan tawagarsa zuwa jam'iyya mai mulki ta APC
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Akwa Ibom – Ndianaabasi Udom, daya daga cikin hadiman Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom, ya ajiye mukaminsa a hukumar kula da hanyoyin karkara a jihar.
Lamarin na zuwa bayan Gwamnan Akwa Ibon, Umo Eno ya yanke shawarar ya yi fatali da PDP da ta shafe shekaru tana mulkin jihar, zuwa APC da ke mulkin kasa a yanzu.

Source: Facebook
Udom ya wallafa takardar murabus dinsa a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 30 ga Satumba, wadda aka rubuta kuma aka tura zuwa ofishin gwamnan.
Hadimin Gwamnan Akwa Ibom ya bar aiki
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa Ndianaabasi Udom ya ajiye aiki ba tare da sanar da ainihin abin da ya sanya shi ya dauki matakin ba.
A takardar ajiye aiki da Udom ya aika wa Gwamna, ya ce:
"Don Allah a karɓi takardar murabus ɗina tare da asalin takardar nadin aiki na, wadda aka sanya ranar 21 ga Yuni, 2023, kuma ta fara aiki daga 1 ga Yuni, 2023."
Udom, ya kasance cikin hadiman farko da Umo Eno ya nada bayan hawansa mulki kuma ana ganin yana da kusanci da Gwamnan jihar.
A baya, ya rike mukamin mataimaki na musamman kan harkokin kungiyoyi da tallafin kasa da kasa a gwamnatin Emmanuel da ta shude.
Dallilin hadimin Gwamna Akwa Ibom na ajiye aiki
Ko da yake Udom bai bayyana dalilin barinsa aiki ba, ana kyautata zaton hakan na da nasaba da rikicin siyasa da ke kara ta’azzara a jihar ba.
Rikicin ya kara kamari bayan sauya shekar Gwamna Eno daga PDP zuwa APC a watan Yuni 2025 — wanda ya kawo karshen fiye da shekaru 20 na mulkin PDP a jihar mai arzikin mai.

Source: Twitter
Sai dai tsohon shugaban PDP na jihar, Aniekan Akpan, ya ki sauka daga kujerarsa, yana mai zargin PDP ta kasa da sabawa dokokinta.
Gwamnan Akwa Ibom zai samar da wutar lantarki
A baya, mun wallafa cewa gwamnan jihar Umo Eno ya rattaba hannu kan yarjejeniya da REA domin samar da wutar lantarki na awa 24, musamman a karkara da ke Akwa Ibom.
Gwamna Eno ya ce hadin gwiwar da aka kulla da REA za ta taimaka wajen saukaka matsalolin da jama’a ke fuskanta sakamakon karancin wuta, duk da arzikin Najeriya.
Da yake zantawa da manema labarai a filin jirgin sama na Victor Attah International Airport bayan dawowarsa daga kasar Birtaniya, Gwamna Eno ya ce za a samu haske a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

