Majalisar Wakilai Ta Fadi Irin Zaben da Shugaba Tinubu Ya ke So a 2027

Majalisar Wakilai Ta Fadi Irin Zaben da Shugaba Tinubu Ya ke So a 2027

  • Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce Bola Tinubu na da niyyar tabbatar da gaskiya da inganci a zabukan 2027
  • Majalisar dokoki na aiki kan sauya dokar zabe ta 2022 domin magance matsalolin da aka fuskanta a shekarar 2023
  • Rahotanni sun nuna cewa Hon. Tajudeen Abbas ya yi wannan maganar ne yayin ganawa da shugabannnin EU a Abuja

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na da niyyar ganin zabukan 2027 sun fi na 2023 inganci.

Rt. Hon. Abbas Ya ce gwamnatin tarayya na da nufin inganta tsarin dimokuraɗiyya ta hanyar zabe mai inganci.

Tinubu tare da shugaban majalisar wakilai
Bola Tinubu tare da shugaban majalisar wakilai. Hoto: Bayo Onanuga|Abbas Tajudeen
Source: Twitter

The Cable ta rahoto cewa ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya karɓi tawagar Tarayyar Turai a Abuja.

Kara karanta wannan

Kudirin sauya tsarin zaben Najeriya na kara ƙarfi a majalisa, an fadi amfanin da zai kawo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abbar Tajudeen ya bayyana cewa majalisar dokoki ta fara sauye-sauye a dokar zabe ta 2022 domin tabbatar da tsarin da zai dace da ƙa’idodin ƙasa da ƙasa.

Shirin majalisar kan sauye-sauyen zabe

Abbas ya bayyana cewa majalisar dattawa da ta wakilai sun gana makon da ya gabata domin daidaita gyare-gyaren da ake son aiwatarwa.

Ya kara da cewa majalisar na da muhimmiyar niyya wajen ganin an samar da dokoki da zasu bai wa hukumar INEC kayan aiki da damar gudanar da ingantaccen zabe.

Sauye sauyen zabe da za a yi

Shugaban majalisar ya bayyana cewa daga cikin sauye-sauyen da ake nazari a kansu akwai samar da kujerun wakilai na musamman ga mata da masu bukata ta musamman.

Haka kuma, ana son bai wa sarakunan gargajiya matsayi a kundin tsarin mulki tare da samun cikakken ikon gudanar da harkokinsu.

Haka zalika, akwai shirin gudanar da dukkan zabubbuka a rana guda – daga shugaban ƙasa, majalisar dokoki, gwamnoni, har zuwa majalisun dokoki na jihohi.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi magana kan sahihancin zaben 2027 da tawagar tarayyar Turai

A cewar Hon. Abbas, wannan zai rage wahalar gudanar da zabe tare da ƙara yawan masu kada kuri’a a Najeriya.

Rokon Najeriya ga tarayyar Turai

Abbas ya bukaci tawagar tarayyar Turai da ta ci gaba da bayar da goyon baya, musamman wajen wayar da kan jama’a kan muhimancin gyare-gyaren.

Ya ce majalisar za ta tabbatar da duk abin da ya shafi doka domin bai wa INEC kayan aiki da ingantattun tsare-tsare don gudanar da zabe mai kyau a 2027.

Atiku yayin ganawa da tawagar EU a Abuja
Atiku yayin ganawa da tawagar EU a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

A cewarsa, hadin gwiwa za ta tabbatar da cewa zabukan gaba za su samu amincewar al’umma, kuma za su kasance bisa ingantattun ka’idojin kasa da kasa.

Atiku ya yi magana kan zaben 2027

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi magana kan zaben Najeriya.

Atiku ya yi magana ne yayin wata ganawa da ya yi da wakilan tarayyar Turai da suka ziyarce shi a Abuja.

Ya yi korafi da cewa har yanzu majalisar kasa da hukumar INEC ba su aiwatar da gyaran da ya kamata ba bayan zaben 2023.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng