Sheikh Triumph Ya Cigaba da Wa'azi a Kano bayan Cewa an Hana Shi, Lauya Ya Magantu
- Barista Ishaq Adam Ishaq ya bayyana cewa ba a hana Sheikh Abubakar Lawan Shua’ibu Triumph yin karatu a jihar Kano ba
- Lauyan ya bayyana cewa ya tattauna da wani dan kwamitin shura da ya ga ana yada jita jitar cewa an hana malamin karatu
- Bincike Legit ya nuna cewa Lawal Shua’ibu Triumph ya ci gaba da karanta wasu littattafan an da ya saba duk da dambarwar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Rahotanni da suka yi yawo a kwanakin baya sun nuna cewa an dakatar da Sheikh Abubakar Lawal Shua’ibu Triumph daga yin karatu a Kano.
Matakin da aka ce gwamnatin jihar ce ta dauka ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin mabiyansa da kuma al’umma gaba ɗaya.

Source: Facebook
Sai dai Barista Ishaq Adam Ishaq ya fito fili ya karyata wannan ikirari a wani bidiyo da aka wallafa a shafinsa na Facebook.
Maganar Barista Ishaq kan lamarin
Barista Ishaq Adam ya bayyana cewa lokacin da aka yi jita jitar ba ya gari, amma daga baya ya kira daya daga cikin ‘yan kwamitin shura ya tambaye shi.
Sheikh Ishaq Adam ya bayyana cewa dan kwamitin shuran ya tabbatar masa cewa ba a hana Sheikh Lawal Triumph karatu ba.
Ya ce, abin da aka tattauna kawai shi ne cewa hana shi maganar kan abin da ake dambarwa a kansa, amma ba ya nufin dakatar da malamin daga yin sauran karatuttukansa.
Baristan ya yi nuni da cewa kwamitin shura ba kotu ba ne, don haka ba shi da hurumin dakatar da wani malami daga gabatar da darusa.
Lawal Triumph zai cigaba da wa'azi a Kano
A cewar Barista Ishaq, Sheikh Lawal zai cigaba da gudanar da karatuttukan da ya saba kamar Umadatul Ahkam, Jawahirul Ma’ani, Tafsiri da kuma Riyadussalihin.
Ya ce babu wanda zai hana shi cigaba da wannan aiki, saboda karatu babban haƙƙi ne na kowane ɗan adam wanda doka ta tabbatar.

Kara karanta wannan
Sheikh Triumph: Guruntum ya magantu kan zargin batanci, ya yi kira ga Gwamna Abba

Source: Facebook
Lawan Triumph ya cigaba da wa'azi?
Mun bibiyi shafukan sada zumunta na Sheikh Lawan, inda muka tabbatar cewa ya cigaba da gabatar da darussa kamar yadda ya saba a Facebook.
Sai dai karatun da ya gudanar a daren Alhamis, 2 ga Oktoban 2025 a yanar gizo ya yi kamar yadda ya saba yi, ba a zahiri cikin masallatai a Kano ba.
Me ya jawo dambarwar a Kano?
Tun da farko wasu matasa a Kano sun gudanar da zanga-zanga, inda suka shigar da ƙorafi ga gwamnatin jihar kan zargin cewa Sheikh Triumph ya yi batanci.
Gwamnatin jihar ta mika batun ga majalisar shura don gudanar da bincike da nazari, domin tabbatar da zaman lafiya da adalci a cikin al’umma.
Wannan shi ne asalin abin da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin mabiyan malamin da sauran jama’a da ya kai ga hana malamin magana kan wasu abubuwa.
Maganar Sheikh Guruntum kan lamarin

Kara karanta wannan
Da sauran rina a kaba: Gwamna Abba ya yi maganar cikar Najeriya shekara 65 da 'yanci
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya yi magana kan abin da ya faru da Sheikh Lawal Triumph.
Malamin ya yi kira ga gwamnatin Kano ta yi adalci wajen bincike da tabbatar da cewa gaskiya ta yi halinta.
A karshe, Sheikh Guruntum ya bukaci masu neman tayar da fitina da cewa za su dauki doka a hannu da su hakura su bar doka ta yi aikinta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
