Rikicin Sarautar Zazzau Ya Dawo Sabo a Kotu, Kalaman Sarki Sun Sake Jefa Shi a Matsala
- Rikicin sarautar Zazzau ya koma kotu, bayan wasu daga cikin dangin sarauta sun shigar da kara kan kalaman da Sarki ya yi
- Dr Nasiru Bashari Aminu da tsohon Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu, suna zargin kalaman Sarkin sun bata mutuncinsu da martabar marigayi Iya
- Za a fara sauraron shari’ar a ranar 4 ga Nuwambar 2025, inda ake sa ran za ta jawo cece-kuce kan martaba da tunanin jama’a
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Zazzau, Kaduna - Rikicin masarautar Zazzau ya dawo bayan kalaman da Sarki, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya yi.
Rikicin ya biyo bayan gadon sarautar Zazzau na 2020, bayan dangin sarauta sun kai karar Sarkin.

Source: Facebook
Rahoton Leadership ya ce ɗan marigayi Iyan Zazzau, Dr Nasiru Bashari Aminu ya shigar da kara yana zargin Sarkin ya yi kalaman batanci kan mahaifinsa.

Kara karanta wannan
Hare hare da kona fadarsa ya tilastawa Sarki tserewa Kamaru, mutanensa sun bi shi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hirar Sarkin Zazzau da ta ta da kura
Hakan ya biyo bayan wata hira da Sarkin ya yi inda ya tabo batutuwa da dama da suka shafi nadin sarauta a masarautar Zazzau.
A hirar da ya yi da RFI Hausa da Legit Hausa ta bibiya, Bamalli ya bayyana yadda ya samu sarauta da wasu ke ganin kalamansa a hirar za su jawo matsaloli.
Mai martaba ya yi maganar yadda aka zabe shi da irin tirka-tirkar da aka yi kuma ya ambaci sunan wasu sarakai a hirar da aka rika fito da su a duk mako.
A bidiyon har ila yau, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli ya umarci fadawansa da su koma makarantar Islamiyya don su gyara addininsu.
Ya bayyana cewa wannan yana daga cikin matakin sauke nauyin da Allah Subhanahu wa ta'ala ya dora masa na jama'arsa.

Source: Facebook
Yaushe kotu za ta fara sauraron karar?

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta yi martani kan zargin jefa 'yan Najeriya miliyan 15 a bakin cikin talauci
A cewar dangin, kalaman sun bata mutuncin marigayin da bai taba zagin masarauta ba, sai dai ya umurci ’ya’yansa su yi biyayya ga sabon Sarki.
Rahotanni daga kotu sun tabbatar cewa an tsara fara shari’ar ranar 4 ga Nuwambar 2025, a Babban Kotun Kaduna, sashen Zariya.
Tsohon Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu, shi ma ya shigar da kara yana kalubalantar kalaman da Sarkin ya bayyana shi a matsayin “mai girman kai”.
Masu nazarin shari’a sun yi gargadi cewa kalaman Sarkin na iya illata martabar masarauta, kasancewar an yada su a rediyo na kasa da kasa, cewa rahoton The Guardian.
Dangin marigayi Iya sun jaddada cewa, ko da ya fi kowa kuri’u daga masu zabe, bai taba nuna rashin girmamawa ga masarauta ba.
Yanzu, shari’ar da ke tsakanin manyan kusoshin masarautar ta koma tsakanin kare mutunci da kuma karfin iko a cikin al’umma.
Majalisa ta samu korafin tsige Sarkin Zazzau
Mun ba ku labari a baya cewa rikici ya sake kunno kai a masarautar Zazzau bayan majalisar dokokin Kaduna ta karɓi ƙorafin cire Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli.

Kara karanta wannan
Kurunkus: Kotu ta yanke hukunci kan ingancin dokar ta bacin da Tinubu ya sa a Ribas
Tsohon Waziri, Ibrahim Muhammad-Aminu, ya zargi Nasir El-Rufai da sabawa doka da al’ada wajen nada Bamalli ba tare da bin tsarin masarauta ba.
Alhaji Ibrahim ya roƙi majalisa ta dawo da shi matsayinsa, ta soke nadin Bamalli kuma ta biya shi duk hakkokinsa da aka dakatar da su.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng