Matasa Sun Yi Zanga Zangar Tir da Kalaman Gwamnan Kano na a Cire Kwamishinan 'Yan Sanda

Matasa Sun Yi Zanga Zangar Tir da Kalaman Gwamnan Kano na a Cire Kwamishinan 'Yan Sanda

  • Ƙungiyar mata lauyoyi ta gudanar da zanga-zanga a Kano bayan kalaman Gwamna Abba Kabir Yusuf a kan Kwamishinan 'yan sanda
  • A ranar 1 ga watan Oktoba, 2025 ne Gwamna Abba ya bayyana takaici da zargin CP Ibrahim Adamu Bakori da ci masa da sauran Kanawa fuska
  • Ya bukaci da a canja Kwamishinan 'yan sandan bisa zarin zama koren wasu daban a maimakon gudanar da aikinsa yadda ya dace

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – A ranar Alhamis, mata lauyoyi a ƙarƙashin inuwar Women Lawyers Congress ta jagoranci gudanar da zanga-zanga a titin Tukur da ke jihar Kano.

A yayin tattakin da su ka yi, sun yi kira ga Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, da kada ya saurari kiran Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

Triumph: An shawarci Abba game da kalaman mataimakinsa, Sagagi kan zargin taba annabi

An yi zanga-zanga a Kano
Hoton wasu daga cikin wadanda su ka yi zanga-zanga a Kano Hoto: Mustapha Muhammad Kankarofi
Source: UGC

Daily Trust ta ruwaito yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana takaici da zargin cewa son rai da biye wa wasu ya hana Kwamishinan ‘Yan Sanda, Ibrahim Adamu Bakori zuwa bikin 'yancin kai.

An yi zanga-zanga a jihar Kano

Solacebase ta wallafa cewa Shugabar ƙungiyar mata lauyoyi, Barrista Nafisa Abba Isma’il, ta bayyana cewa wannan buƙatar ta gwamna ba ta da tushe face siyasa.

Ta kara da cewa haka kuma na iya dagula tsaron jihar Kano bayan ana samun zaman lafiya da kwanciyar hankali saboda aikin Kwamishinan.

A cewarta:

“A lokacin da al’amuran tsaro a jihar ke cikin barazana, irin wannan mataki na kara kawo alamar tambaya kan niyyar waɗanda ke riƙe da madafun iko.”

Ƙungiyar ta zargi Gwamna da kin baiwa 'yan sanda hadin kai, har ma da watsi da buƙatar mataimakin IGP da ke son ganawa da shi kan batun tsaro.

Nabila ta ƙara bayyana cewa sakin fiye da mutane 300 da ake zargin ‘yan daba ne a lokacin zaɓen raba gardama a Kano ya zama misalin yadda siyasa ke lalata tsarin doka a jihar.

Kara karanta wannan

A maida wukar: NNPP ta tsoma baki a sabanin Gwamnan Kano da Kwamishinan 'yan sanda

Jama'a sun goyi bayan Kwamishinan Kano
Hoton wasu daga cikin wadanda su ka yi zanga-zanga a Kano Hoto: Mustapha Muhammad Kankarofi
Source: UGC

Ta yi gargadi cewa yawaitar kungiyoyin daba, satar akwatin zaɓe, da makamantansu na ci gaba da barazana ga rayukan al’umma.

Kungiya ta nemi a yi bincike a Kano

A gefe guda kuma, wata ƙungiyar farar hula mai suna One Kano Agenda ta bukaci gwamnatin tarayya ta gudanar da bincike kan janye jami’an ‘yan sanda daga bikin cikar Najeriya shekaru 65 a Kano.

Jagoran ƙungiyar, Kwamredd Abbas Abdullahi Yakasai, ya bayyana wa taron manema labarai cewa abin da ya faru ya zubar da darajar bikin samun ‘yanci kansa.

Ya bukaci gwamnati ta hukunta duk wanda ya yi rawar gani a wannan lamari, yana gargadin cewa bai kamata a bari siyasa ta ruguza manyan bukukuwan ƙasa da suka shafi kowa ba.

Jama'a sun fusata a Kano

Wasu da su ka sanya da Legit sun shaida yadda su ke ganin ana samun matsala a tsakanin rundunar ƴan sandan Kano da gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Abba ya jero bangarori 5 da gwamnatin Kano ta farfado da su a cikin shekaru 2

Aminu Abdullahi Ibrahim, guda daga cikin ƴan jaridan gidan gwamnati kuma mai sharhi a kan al'amuran siyasa ya ce:

"Za mu iya cewa abin da ya faru a ranar bikin samun ƴancin Najeriya abu ne da bai yi dadi ba."
"Kuma za a iya cewa raini ne ga shi Gwamnan Jihar Kano, raini ne ga kundin tsarin mulki kuma raini ne ga al'ummar Kano baki daya."

Aminu Abdullahi ya ce an kammala tsari a kan yadda za a gudanar da bikin, amma ana dab da fara bikin, aka nemi jami'an yan sanda aka rasa.

Ya ce sun yi tsammanin ko da matsala ce ta hana yan sandan zuwa, ya kamata Kwamishinan yan sanda Ibrahim Adamu Bakori ya sanar da Gwamna Abba Kabir.

Gwamnan Kano ya aika sako ga ma'aikata

A baya, mun wallafa cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci jami’an gwamnatinsa da masu rike da mukaman siyasa da su jajirce wajen sauke nauyin da ya rataya a kansu.

A wata sanarwa da mai magana‑da‑yawun gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bukaci su dabbaka aikinsu a kan shawarwari na gaskiya da rikon amanar jama'ar da ake wakilci.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya kinkimo aikin da aka kwashe shekara 50 ana alkawarin yi a Kaduna

Gwamna Abba ya ce bai kamata a ci amanar mutanen da suka ba shi kuri’unsu a zabukan 2023 ba, kuma ya yi gargadi kan matsalar cin hanci da rashawa, domin yana cutar da talakawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng