Yayin Ganawa da Turawa, INEC Ta Fadi Matsalar da za Ta iya Shafar Zaben 2027
- Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, ya bukaci majalisar tarayya ta gaggauta kammala gyaran dokokin zabe kafin babban zaben 2027
- Farfesa Mahmood Yakubu ya ce rashin tabbas kan gyaran dokar na iya dagula shirin hukumar yayin da zabe ke kara karatowa
- Ya bayyana hakan ne yayin taro da shugabannin tawagar EU da suka zo duba aiwatar da shawarwarin da suka bayar bayan zaben 2023
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban hukumar zabe (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu, ya bukaci majalisar dokokin tarayya da ta hanzarta amincewa da gyare-gyaren dokokin zabe.
Ya bayyana haka ne yana mai cewa gyaran zai inganta shirin hukumar kafin babban zabe na 2027.

Source: Facebook
The Cable ta rahoto cewa ya yi wannan bayani ne a ranar Alhamis, 2, Oktoba, 2025, lokacin da ya karbi bakuncin shugaban tawagar sa ido ta Tarayyar Turai (EU), Barry Andrews.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shawarwarin EU da amsar hukumar INEC
Yakubu ya bayyana cewa hukumar ta yi nazari sosai kan shawarwarin da EU ta bayar a rahotonta na zaben 2023, inda aka lissafa shawarwari 23 gaba ɗaya.
Ya ce cikin wannan adadi, an miƙa shawarwari takwas kai tsaye ga INEC, ɗaya daga ciki aka ayyana a matsayin mai muhimmanci.
Haka zalika, sauran shawarwari 15 da aka bayar sun shafi gwamnati, jam’iyyun siyasa, majalisa, kotu, da sauran masu ruwa da tsaki a harkar siyasa.
Korafin INEC kan shirin zaben 2027
Shugaban INEC ya jaddada cewa zabe tsari ne da doka ke jagoranta, don haka yana da matukar muhimmanci a tabbatar da gyaran dokokin tun kafin a shiga babban zabe.
Ya ce jinkiri wajen kammala gyaran dokokin zai iya kawo cikas ga shirye-shiryen INEC, musamman idan zabe ya matso ba tare da an tabbatar da tsarin shari’a ba.
Ya bayyana cewa hukumar ta dauki matakan aiwatar da shawarwarin da ke bukatar sauye-sauyen gudanarwa, kana tana aiki tare da sauran hukumomi kan sauran shawarwari.

Source: Facebook
EU ta nemi karin bayani daga INEC
A nasa bangaren, shugaban tawagar EU, Barry Andrews, ya ce sun ziyarci Najeriya ne domin tantance irin ci gaban da aka samu wajen aiwatar da shawarwarin da suka bayar.
Ya ce suna son jin ainihin matakan da aka dauka, matsalolin da suka rage, da kuma kalubalen da za su iya tasowa musamman kan gyaran kundin tsarin mulki da na gudanarwa.
Rahoton Channels TV ya nuna cewa Andrews ya nuna farin cikinsa da yadda aka samu ci gaba, duk da cewa akwai karancin lokaci wajen aiwatar da cikakkun sauye-sauye.
Ana cigaba da rajistar zabe a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar INEC ta fitar da rahoto game da rajistar masu kada kuri'a da aka shafe mako shida ana yi.
A bayanan da hukumar INEC ta fitar, jihar Borno ce ke kan gaban dukkan jihohin Najeriya yayin da Osun ke binta a baya.
Jihar Legas ce ta zamo ta uku a yawan masu rajista yayin da jihar Kaduna ta samu jama'a sosai, amma Ogun ta wuce Kano da Gombe.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


