Gwamna Ya Bukaci Diyyar N100bn bayan Tsohon Kwamishina Ya Kira Shi Barawo a Facebook

Gwamna Ya Bukaci Diyyar N100bn bayan Tsohon Kwamishina Ya Kira Shi Barawo a Facebook

  • Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya nuna damuwa kan yada wasu bayanai a manhajar Facebook da ke zubar masa da mutunci
  • Alex Otti ya nemi diyya ta Naira biliyan 100 daga tsohon kwamishina, Eze Chikamnayo kan wallafe-wallafen bata suna
  • Lauyan gwamnan ya ce rubuce-rubucen suna nufin nuna kiyayya da ɓata martabar Otti, wanda ya ce ba a taba tuhumarsa a kotu ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Umuahia, Abia – Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya gagara yin hakuri kan wasu rubuce-rubuce da aka yi game da shi a Facebook.

Gwamna Otti ya bukaci tsohon kwamishinan yada labarai na jihar, Eze Chikamnayo, ya biya shi diyyar Naira biliyan 100.

Gwamna zai dauki mataki kan cin zarafinsa a Facebook
Gwamna Alex Otti na jihar Abia a gidan gwamnati. Hoto: Alex C. Otti.
Source: Facebook

Gwamna ya fusata kan bata masa suna a Facebook

Rahoton TheCable ya ce gwamnan ya bukaci haka ne a matsayin diyya kan zargin bata masa suna a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Abba ya jero bangarori 5 da gwamnatin Kano ta farfado da su a cikin shekaru 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata wasiƙa daga lauyan gwamnan, Sonny Ajala (SAN), ta ce Chikamnayo ya wallafa kalaman da ke cike da cin mutunci da zage-zage.

Daga cikin kalmomin da aka yi amfani da su akwai “Alex Otthief is a confirmed criminal and congenital liar” (Alex barawo ne, mai laifi kuma makaryaci) da wasu makamantansu.

Ajala ya ce rubuce-rubucen a Facebook sun janyo masa mummunar illa, ciki har da damuwa, bakin ciki da zubewar mutunci da ya gina cikin shekaru.

“Domin kauce wa shakku, wanda muke karewa, shi ne kaɗai gwamna kuma babban jami’in gudanarwa na wata jiha cikin jihohi 36 na Najeriya da ke ɗauke da suna Alex Chioma Otti.
“Saboda haka babu wani ƙoƙari da ake buƙata daga jama’a wajen bata sunan Otti saboda ƙiyayya, ƙarya da ɓatanci gare shi.
"Hakan bai dace ba ko dai ta hanyar kiran sunansa kai tsaye ko kuma ta wani salo na bambance sunan Alex Chioma Otti ta hanyar barkwanci, misali, alama ko kuma sauya suna.”

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya kinkimo aikin da aka kwashe shekara 50 ana alkawarin yi a Kaduna

Gwamna ya bukaci diyyar N100bn kan zargin bata suna
Gwamnan jihar Abia, Alex Otti yayin wani taro a Umuahia. Hoto: Alex C. Otti.
Source: Twitter

Bukatar gwamna Otti ga tsohon kwamishinan

Gwamnan ya nemi Chikamnayo ya goge wallafe-wallafensa daga Facebook tare da ba da hakuri a jaridu hudu na kasa, haka kuma ya bukaci ya yi rubutun neman afuwa a shafin nasa.

Ya kara da cewa idan bai bi wannan umarni cikin kwana bakwai ba, za a kai shi kotu domin neman hukuncin doka kan abin da ya wallafa, cewar rahoton Vanguard.

Ajala ya jaddada cewa Gwamna Otti bai taba samun tuhuma ko hukuncin kotu ba, kuma mutuncinsa ya kasance mai daraja tun lokacin da yake shugabancin bankin Diamond har zuwa yau.

An soki gwamna kan karbar bashin Musulunci

Kun ji cewa Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya yi karin haske bayan taso shi a gaba kan karbar bashin bankin Musulunci.

Gwamna Otti ya bayyana cewa an amince da bashin dala miliyan 125 daga Bankin Raya Musulunci domin ci gaban ayyuka.

Kara karanta wannan

Jerin tsofaffin gwamnonin Najeriya 7 da suka dawo manyan sarakuna

Ya ce za a yi amfani da bashin wajen gine-gine da hanyoyi a Abia, tare da samar da ayyukan yi sama da 3,000 a wurare daban-daban a jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.