Tashin Hankali: Mataimakin Sakataren Jam'iyyar ADC Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce

Tashin Hankali: Mataimakin Sakataren Jam'iyyar ADC Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce

  • Mutuwar ba-zato ta Ugochimereze Chinedu Asuzu, Mataimakin PRO na ADC Imo, ta girgiza jama’a, inda jam’iyya ta bayyana shi a matsayin babban rashi
  • Asalin dan Umuma Isiaku, Ideota ta Kudu, marigayi ya kasance mu’assasin kungiyoyi da dama, ciki har da Ikoro Ndigbo da I Stand With ADC
  • Jam’iyyar ADC ta ce za ta sanar da lokacin jana’izarsa daga baya, tana mai cewa sadaukarwar da ya yi ba za ta taba gushewa ba a siyasar Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Imo - Jam'iyyar ADC ta shiga cikin tsananin jimami biyo bayan rasuwar mataimakin sakataren hulda da jama'a na jam'iyyar a jihar Imo.

An ruwaito cewa, mataimakin sakataren hulda da jama'ar na ADC, Hon. Ugochimereze Chinedu Asuzu ya yi mutuwar fuju'a, wadda ta girgiza jama'a.

Jam'iyyar ADC ta rasa mataimakin sakatarenta na bangaren hulda da jama'a a Imo
Dama zuwa Hagu: Malam Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi, Atiku Abubakar, David Mark, Rau'uf Aregbesola, a taron kaddamar da ADC a Abuja. Hoto: @atiku
Source: Facebook

Mataimakin sakataren ADC ya mutu

Kara karanta wannan

Sokoto, Kebbi da jihohin Arewa 5 za su fuskanci ambaliya, gwamnati ta yi gargadi

Kafin mutuwarsa, Ugochimereze ya kasance mu'assasin kungiyar Ikoro Ndigbo, kuma jagora a harkokin da suka shafi Inyamurai, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna cewa, Ugochimereze ya yanke jiki ne ya fadi matacce a safiyar ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba, 2025.

Sakataren watsa labarai da hulda da jama'a na jam'iyyar ADC, jihar Imo, Chief MacDonald Amadi, ya sanar da mutuwar Ugochimereze a sanarwar da ya fitar.

A cikin sanarwar, ADC ta bayyana mutuwar Ugochimereze a matsayin babban abin takaici, tana mai cewa ya sadaukar da rayuwarsa ga hidimtawa al'umma.

Nasaba da tarihin gwagwarmayar jigon ADC

Dan asalin garin Umuma Isiaku da ke karamar hukumar Ideota ta Kudu, Ugochimereze ya samu ilimin boko mai zurfi kuma ya jima a fafutukar siyasa.

Ugochimereze ya yi karatun digiri a fannin fasahar addini da siyasa, kuma ya mutu ne a sa'ilin da yake karatun digiri na biyu.

Baya ga siyasa, shi masani ne kan addini, kasuwanci, yada al'adu da kuma mai rajin kare muradun Inyamurai, in da ya samar da kungiyar IIR, wacce ke yada al'adun kabilar.

Kara karanta wannan

Ganduje ya hadu da shugaban kasa, Tinubu ya magantu kan zargin kisan Kiristoci

Shi ne kuma ya assasa tare da zama shugaban I Stand With ADC na kasa, wata gamayyar kungiyoyin da ke fafutukar hada kan jama'a don zaben ADC.

ADC ta ce ba za a samu madadin mataimakin sakatarenta na hulda da jama'a da ya rasu nan kusa ba
Taswirar jihar Imo da ke a Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

ADC ta yi jimamin rashin jigonta a Imo

Tsohon jigo a babbar jam'iyyar adawa ta PDP, Ugochimereze ya kasance kwararren marubuci, mai sharhi kan lamuran yau da kullum, kuma malamin jami'a.

Sanarwar ta kara bayyana shi a matsayin uba, miji, kuma abin koyi, wanda yake da kyakkyawar fahimta ga mabiya addinai daban daban.

"Ba za a taba samu madadin Chief Asuzu ga iyalansa, jam'iyyar ADC da kuma kasa baki daya, domin sadaukarwa da jajurcewarsa."

- Chief MacDonald Amadi.

Sanarwar ta ce nan gaba kadan za a sanarwa al'umma lokacin da za a yi bikin binne gawar mataimakin sakataren hulda da jama'a na ADC, Ugochimereze Chinedu Asuzu.

Ana shirin dakile farin jinin ADC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban jam'iyyar ADC na ƙasa, Sanata David Mark, ya yi zargi kan gwamnatin jam'iyyar APC.

David Mark ya nuna cewa akwai shirin da gwamnatin za ta yi domin ganin ta dusashe tauraruwar ADC wadda ke haskawa a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Nigeria @65: Jawabin da Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya a yau 1 ga Oktoba 2025

Kalamansa na zuwa ne bayan an samu wasu lauyoyi da suka shirya kare jam'iyyar a kowace shari'a a faɗin Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com