Rikicin Shugabanci: Jami'an Tsaro Sun Mamaye Ginin Sakatariyar Jam'iyyar PDP

Rikicin Shugabanci: Jami'an Tsaro Sun Mamaye Ginin Sakatariyar Jam'iyyar PDP

  • Jami’an tsaro sun mamaye sakatariyar PDP a Akwa Ibom bayan rushewar kwamitin gudanarwa na jihar da NWC ta yi
  • Shugaban PDP da aka tsige, Aniekan Akpan, ya ce an kori kwamitin gudanarwarsa ba bisa ka’ida ba ne, don haka suna nan daram
  • Aniekan Akpan ya jaddada biyayyarsa ga Gwamna Umo Eno a matsayin shugaba ga kowa a jihar duk da ya koma jam'iyyar APC

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Akwa Ibom - Rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaro sun mamaye sakatariyar jam'iyyar APC a jihar Akwa Ibom a ranar Alhamis.

An rahoto cewa jami'an tsaron sun yi mamayar ne don hana tashin hankali bayan rikicin cikin gida a jam’iyyar PDP ya kara tsamari.

Jami'an tsaro sun mamaye sakatariyar PDP a Akwa Ibom
Sabuwar sakatariyar jam'iyyar PDP da aka gina a birnin Uyo, jihar Akwa Ibom. Hoto: Native Reporters
Source: Facebook

Akwa Ibom: Rikicin shugabanci ya shiga PDP

Wannan na zuwa ne bayan sanarwar rushe shugabannin PDP na jihar da kwamitin NWC na jam'iyyar ya fitar, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

A maida wukar: NNPP ta tsoma baki a sabanin Gwamnan Kano da Kwamishinan 'yan sanda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun PDP na kasa, Debo Ologunagba, ne ya bayyana cewa an kori shugabannin kuma an nada kwamitin rikon kwarya mai mambobi 31.

Sai dai sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya fito da wata sanarwa daban yana cewa babu wani taron NWC da ya yanke irin wannan hukunci.

Shugaban PDP a Akwa Ibom da aka tsige, Aniekan Akpan, ya bayyana cewa an rushe shugabancinsu ba bisa ka’ida ba.

Shugaban PDP da aka tsige ya yi martani

Aniekan Akpan ya kara da cewa kwamitin shugabancinsa yana nan daram har sai sun kammala wa’adin mulki na shekaru hudu.

Akpan ya zargi wasu ‘yan jam’iyyar da kokarin rusa PDP a jihar, yana mai cewa jam’iyyar tana tafiya ne bisa tsarin doka da kundin tsarin mulki.

Ya bayyana hakan ne a ganawarsa da manema labarai a ranar Alhamis, tare da dukkan mambobin da ake zargin an tsige, inji rahoton The Sun.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Yadda wani shugaban APC ya mutu yana cikin raba N50,000

Akpan ya kara da cewa wasu daga cikin shugabannin da aka zaba cikin sabon kwamitin rikon kwarya sun ce an yi hakan ba tare da yardarsu ba, hakan ya nuna rashin gaskiyar lamarin.

Akpan ya ce babu wani taron NWC da ya tattauna kan tsige su, inda ya nuna cewa sakataren PDP na kasa ya riga ya fitar da sanarwa don fayyace matsayinsu na doka.

Yanzu dai rikici ya mamaye PDP a Akwa Ibom kan rushe shugabannin jam'iyyar
Taswirar jihar Akwa Ibom da ke a Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Akpan na tare da gwamnan da ya koma APC

Ya bukaci magoya baya da jama’a su yi watsi da rahotannin da aka yada a baya, su kuma goya wa kwamitin shugabancinsu, wanda shi ne halastacce a jam’iyyar.

Shugaban PDP din ya kuma jaddada cewa shi da abokan aikinsa za su ci gaba da kasancewa tare da Gwamna Umo Eno, wanda ya ce shugaba ne ga dukkan ‘yan jihar ba tare da la’akari da jam’iyya ba.

“A matsayinsa na gwamna, Gwamna Umo Eno na wakiltar kowa, kuma ba za a iya cewa mun aikata cin amanar jam’iyya saboda kusanci da shi ba."

- Aniekan Akpan.

'Yan sanda sun mamaye sakatariyar PDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rikici ya barke a PDP ta jihar Rivers yayin da ‘yan sanda suka toshe hanyar zuwa sakatariyar jam’iyyar.

Kara karanta wannan

PDP ta rusa dukkanin shugabanninta a jihohi 2, ta nada kwamitin riko

Rahoto ya nuna cewa 'yan sanda sun je dakile tarzoma ne bayan da aka ji cewa wani tsagi na jam'iyyar zai kwace iko da sakatariyar.

Rikicin jam'iyyar dai ya kara tsananta ne yayin da bangarorin biyu ke nuna iko da shugabanci bayan hukuncin kotu kan sahihin kwamitin gudanarwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com