An Rage Mugun Iri: Sojojin Sun Sada Hatsabibin Dan Bindiga da Yaransa da Mahaliccinsu

An Rage Mugun Iri: Sojojin Sun Sada Hatsabibin Dan Bindiga da Yaransa da Mahaliccinsu

  • Gwamnatin jihar Kwara ta tabbatar da mutuwar daya daga cikin jagororin masu garkuwa da mutane bayan farmakin sojoji
  • Hukuma ta ce Maidawa ya bakunci lahira bayan luguden wuta na dakarun rundunar sojin sama a dazukan Isanlu-Isin
  • Rahotanni sun ce Maidawa da wasu daga cikin yaransa sun mutu yayin artabu da jami’an tsaro a iyakar Kwara da Kogi, bayan kiran gaggawa daga gwamnati

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin, Kwara – Gwamnatin jihar Kwara ta tabbatar da harin rundunar sojojin sama da ya yi ajalin tantirin dan bindiga wanda ya addabi al'umma da dama.

Gwamnatin ta bayyana cewa fitaccen jagoran masu garkuwa da mutane a yankin, wanda aka fi sani da Maidawa, ya mutu sanadin harin da aka musu.

An hallaka tantirin dfan bindiga a Kwara
Gwamnan Kwara, shugaban sojojin sama da dan bindiga da aka hallaka. Hoto: Kwara State Government, Nigerian Air Force HQ.
Source: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan jihar Kwara, Rafiu Ajakaye, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Fusatattun matasa sun kona gidan basarake a Binuwai, sun bayyana dalilinsu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tantirin dan bindiga ya mutu a Kwara

Majiyoyi sun tabbatar da cewa dan bindigan ya mutu bayan luguden wuta da rundunar sojin sama ta Najeriya wanda ya samo asali bayan harin yan bindiga a jihar.

Harin ya faru ne a dazukan Isanlu-Isin da ke Kwara da kuma iyakokin jihar Kogi da suka makwabtaka a Arewa ta Tsakiya a Najeriya.

A cikin sanarwar a yau Alhamis, Ajakaye ya ce jami’an tsaro sun samu nasarar hallaka Maidawa tare da wasu daga cikin yaransa bayan artabu.

Kwara: 'Dan bindiya ya sanar da mutuwar Maidawa

Sanarwar ta ce rahotannin sirri da aka kama sun tabbatar da cewa wani mai garkuwa da mutane da ake nema, Baccujo, ya sanar da sauran abokan aikinsu a Katsina cewa Maidawa ya mutu.

Gwamnatin ta ce samamen tsaro na gudana ne domin fatattakar yan bindiga da ke addabar jama’a da hare-haren, tare da yin garkuwa da mutane domin kudin fansa.

Kara karanta wannan

DSS sun kwace makaman yan sa kai kafin harin yan bindiga? Gwamnati ta magantu

Tantirin dan bindiga ya mutu a kwara
Taswirar jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Mummunan hari da yan bindiga suka kai

Rahotanni sun kara da cewa luguden wutan ya shafi wuraren da ake fama da hare-hare a ’yan makonnin nan, ciki har da Ifelodun, Ekiti, Isin, Edu da Patigi.

An tuna cewa a makon da ya gabata, ’yan bindiga sun kai hari a Oke-Ode, inda suka kashe masu gadin daji 11 da wasu mazauna gari.

Har ila yau, majiyoyi sun ce an yi garkuwa da mutane wanda hakan ya jawo fara luguden wuta mai karfi daga sojoji da rundunar sojin sama.

Gwamnatin Kwara ta musanta kwace makaman 'yan sa-kai

A wani labarin, Gwamnatin Kwara ta yi karin haske kan jita-jitar da ake yadawa bayan yan bindiga sun kai mummanan hari a jihar.

Hukumomi a jihar sun karyata cewa hukumar DSS ta kwace makaman masu gadi a Oke-Ode kafin aka kai hari wanda ya yi sanadin mutuwar yan sa-kai da dama yayin farmakin.

Kara karanta wannan

Saura Turji: 'Yan sanda sun cafke tantirin dan bindiga a Zamfara

Harin da aka kai ya yi sanadiyyar mutuwar masu gadi 12 tare da yin garkuwa da wasu mazauna gari da ba su san komai ba wanda ya fara sanya shakku kan hanyar magance matsalar tsaro.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.