Duniya kenan: Tsohon Kwamishina a Gwamnatin APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya tura sakon ta'aziyya bayan babban rashi da jihar ta yi a tsakiyar makon nan
- Inuwa ya bayyana rasuwar tsohon kwamishina Julius Ishaya Lepes a matsayin babban rashi ga jihar da al’ummar Kaltungo baki ɗaya
- Gwamnan ya ce Lepes ya bayar da gudunmawa mai tarin amfani ga APC da majalisar zartarwa lokacin da ya rike kujerar kwamishina a jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe – Jihar Gombe ta yi babban rashi bayan sanar da rasuwar daya daga cikin tsofaffin kwamishinoni a jihar.
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi alhini kan rasuwar tsohon kwamishina a jihar, Julius Ishaya Lepes.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanar da Legit Hausa ta samu daga shafin sakataren yada labaran gwamnan, Isma'ila Uba Misilli a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin Ishaya na barin APC zuwa NNPP
Julius Ishaya ya taba rike mukamin kwamishinan yada labarai a mulkin farko na gwamnatin Muhammadu Inuwa Yahaya wanda ya ba da gudunmawa matuka.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa daga bisani, Julius Ishaya ya yi murabus daga mukaminsa na kwamishina domin yin takara.
Daga bisani, a watan Janairun 2023, Julius Ishaya ya tabbatar da ficewarsa daga APC zuwa jam'iyyar NNPP saboda rashin jan shi a jiki, cewar rahoton Tribune.
Tsohon dan takarar gwamna a NNPP, Khamisu Ahmed Mai Lantarki shi ne ya karbi Ishaya a wancan lokaci domin inganta jam'iyyar.

Source: UGC
Yabon da tsohon kwamishinan ya samu daga Gwamna
Inuwa ya bayyana Lepes a matsayin mutum mai gaskiya da basira, wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunkasar jam’iyyar APC a jihar Gombe.
Ya ce lokacin da Lepes ya yi aiki a matsayin kwamishinan matasa sannan daga baya a matsayin kwamishinan yada labarai da al’adu, ya nuna jajircewa da hangen nesa.

Kara karanta wannan
Bayan Tinubu ya maido shi ofis, Fubara ya dauki mataki mai tsauri a kan kwamishinoninsa
Gwamnan ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi, ba ga iyalan mamacin kadai ba, har da al’ummar Kaltungo da jihar Gombe gaba ɗaya.
Gwamna ya jajantawa al'umma kan rashin Ishaya
A madadin gwamnatin jihar da jama’ar Gombe, Inuwa ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Lepes, abokan aikinsa da al’ummar Kalargu na masarautar Kaltungo.
Ya yi addu’a da neman Allah Madaukaki ya gafarta wa mamacin, ya kuma baiwa iyalansa da sauran al’umma haƙurin jure wannan babban rashi.
An tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne a jiya Laraba 1 ga watan Octoban shekarar 2025 da muke ciki bayan fama da ciwon koda.
Hadimin gwamnan Gombe ya bar duniya
A baya, mun kawo muku cewa Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya bayyana jimaminsa kan rasuwar hadiminsa na musamman a jihar da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Marigayi Mamman Alkali ya rasu a ranar Laraba 23 ga watan Yulin shekarar 2025 a Gombe bayan gajeriyar rashin lafiya da ya sha fama da ita.
Inuwa ya ce Mamman Alkali mutum ne mai amana, hazikin dan siyasa kuma wanda ya yi wa dimokuradiyya hidima na gaskiya da ya sadaukar da kansa wajen hidimar jama’a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
