Rashin Tsaro: 'Yan bindiga Sun Tilasta Rufe Makarantu 180 a Arewa
- Fiye da makarantu 180 aka rufe a jihohin Arewa saboda hare-haren ‘yan bindiga da rikice-rikicen masu alaka da tsaro
- Dubban yara suna yawo ba tare da samun damar yin karatu ba, wasu kuma an tura su sansanonin ‘yan gudun hijira
- Masana ilimi sun yi gargadin cewa wannan matsala za ta kara haifar da jahilci da talauci, musamman a yankunan karkara
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Matsalar rashin tsaro da ta addabi yankin Arewa ta jawo asarar rayuka, arziki, da kuma gagarumar matsala ga ilimi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa makarantu sama da 180 ne aka rufe a jihohi daban-daban saboda hare-haren ‘yan bindiga da ta’addanci.

Source: Getty Images
A binciken da Daily Trust ta yi, jaridar ta gano cewa a wasu makarantun sun zama mafaka ga ‘yan gudun hijira, 'yan bindiga yayin da wasu aka dauke su wajen zama na jami’an tsaro.
Masana ilimi da al’ummar gari sun nuna damuwa cewa tsawon lokacin da yara za su yi a gida ba tare da samun karatu ba, zai kara dagula rayuwarsu tare da haddasa karuwar jahilci da fatara.
Makarantu 39 sun daina aiki a Zamfara
A jihar Zamfara kadai, makarantu 39 ne aka tabbatar da rufe su, ciki har da makarantun firamare 20 da sakandare 19.
A wasu kananan hukumomi irin su Anka, Tsafe, da Kaura Namoda, makarantu sun dade fiye da shekaru shida a rufe.
Rahotanni sun nuna cewa a wasu garuruwa, jami’an tsaro ne suka mamaye makarantun don dakile hare-haren ‘yan bindiga.
Malam Hassan Isa daga Anka ya bayyana cewa:
“Yaranmu da yawa sun daina zuwa makaranta tun shekaru bakwai da suka gabata. Sai dai kadan daga cikinsu aka mayar zuwa wasu makarantu a wasu garuruwa.”
Katsina da Niger: Dubban yara na gararamba
A jihar Katsina, rahoton UNICEF ya nuna cewa yara fiye da miliyan 1.4 ne ba su zuwa makaranta, wanda ya kai kashi 45 cikin 100 na yawan yaran jihar.

Kara karanta wannan
Katsina: Mutane sun yi kukan kura, sun cafke ƴan bindiga da ke taimakon Bello Turji
Premium Times ta fitar da makamancin wannan rahoto tun a farkon shekarar 2024.
A wasu kananan hukumomi irin su Batsari, Faskari da Kankara, makarantu 52 ne aka rufe saboda hare-hare, sai kadan daga cikinsu aka sake budewa.
Haka kuma a jihar Neja, makarantu 30 ne suka daina aiki, ciki har da makarantun firamare 18, sakandare daya.

Source: Getty Images
An rufe makarantu a Sokoto da Kaduna
A Sokoto, makarantu guda shida da suka hada da kwalejin kimiyya da makarantun ‘yan mata sun dade a rufe.
A wasu wurare, al’ummar da rikici ya raba da gidajensu ke kwana a cikin makarantu sannan su bar su da rana don a ci gaba da darasi.
A Kaduna kuwa, wasu garuruwa gaba daya sun zama kufai bayan mutane sun gudu, lamarin da ya bar makarantu da yawa a cikin daji babu kowa.
A Kebbi, har yanzu tsoron sace dalibai ya sa iyaye sun fi son tura ‘ya’yansu makarantu da ke cikin gari.
Tun bayan garkuwar dalibai 96 a Birnin Yauri a shekarar 2021, makarantu da dama sun kasance a kulle.
An rufe makarantu a jihar Benue
A Benue, rahotanni sun nuna makarantu 55 ne aka rufe a shekarar 2024 kadai, inda aka maida su wurin zama na dubban ‘yan gudun hijira.
Wannan ya haddasa matsalar koma baya a bangaren ilimi a yankunan Guma, Logo, Agatu da Gwer West.
Wani rahoto ya ce an kashe mutane fiye da 540 a cikin wata biyu a jihar, lamarin da ya kara tayar da hankalin al’umma tare da hana yara yin karatu.
An harbe tsohon dan bindiga a Benue
A wani rahoton, kun ji cewa wasu mutane sun harbe wani tsohon dan bindiga da ya mika wuya bayan ya tuba.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutane ne a kan babur suka yi amfani da bindiga suka kashe mutumin.
Sai dai jami'an rundunar 'yan sanda sun kaddamar da bincike kan wadanda suka aikata kisan, kuma an kama mutum daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

