A Maida Wukar: NNPP Ta Tsoma Baki a Sabanin Gwamnan Kano da Kwamishinan 'Yan Sanda

A Maida Wukar: NNPP Ta Tsoma Baki a Sabanin Gwamnan Kano da Kwamishinan 'Yan Sanda

  • Jam'iyya mai mulki ta NNPP a Kano ta sa baki bayan Abba Kabir Yusuf ya nuna bacin ransa a kan Kwamishinan ƴan sandan jihar
  • A ranar da aka yi bikin tunawa da samun 'yancin Najeriya, Gwamna Abba ya zargi kwamishinan 'yan sanda, Ibrahim Bakori da son kai
  • A jawabinsa, Shugaban NNPP na Kano, Hashim Dungurawa, ya bukaci bangarorin biyu su daidaita sabani don zaman lafiyar jihar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Shugaban jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya yi magana a kan sabanin da ya ratsa tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da rundunar 'yan sanda.

Ya bukaci Gwamnan da Kwamishinan ƴan sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, da su yi hakuri da juna tare da sasanta sabanin da ya kunno kai tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Abba ya jero bangarori 5 da gwamnatin Kano ta farfado da su a cikin shekaru 2

NNPP ta nemi sulhu tsakanin Gwamna da Kwamishinan 'yan sanda
Hoton Kwamshinan 'yan sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori da Abba Kabir Yusuf Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa/Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Jaridar Leadershio ta wallafa cewa lamarin ya samo asali ne daga yadda Kwamishinan 'yan sandan ya janye dakarunsa daga halartar bikin ranar dimokuradiyya a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPP ta ba Gwamna, kwamishinan 'yan sanda hakuri

Shugaban NNPP, Hashimu Dungurawa ya bayyana cewa rashin jituwa tsakanin manyan shugabannin tsaro da gwamnati ba abin da ya dace ba ne, idan ana son zaman lafiya mai dore wa.

Ya ce:

“A matsayinsa na shugaban tsaro na jiha, gwamna dole ne ya ji cewa ba a mutunta shi ba idan kwamishinan ƴan sanda bai bayyana a wani muhimmin taro kamar haka. Amma ba mu san me ya hana kwamishina zuwa ba. Dole ne a zauna a sasanta."

Dungurawa ya gargadi bangarorin biyu cewa idan suka ci gaba da aiki ba tare da fahimtar juna ba, to lamarin zai kai ga nakasu ga al’ummar jihar.

A kalamansa:

“Idan suka daina aiki tare, tabbas Kano ce za ta yi asara. Duk abin da ya faru ya kamata a yi shi ne domin ci gaban jihar, ba akasin haka ba.”

Kara karanta wannan

Bayan Tinubu ya maido shi ofis, Fubara ya dauki mataki mai tsauri a kan kwamishinoninsa

NNPP ta shawarci Gwamna, Kwamishinan 'yan sanda

Hashimu Dungurawa ya ce matsayinsa na shugaban jam’iyya ba shi da wata manufa sai ganin cewa Kano ta samu zaman lafiya, tsaro da cigaba a jihar.

NNPP ta ce zaman lafiyar Kano ce a kan gaba
Hoton Shugaban NNPP na Kano, Hashimu Dungurawa Hoto: Dr. Hashim Dungurawa
Source: Facebook

Ya ce:

“Ni ina kallon jihar Kano gaba ɗaya, ba wai gwamna ko kwamishinan ƴan sanda kadai ba. Abu mafi muhimmanci shi ne zaman lafiya da jin daɗin mutanen jihar. Ya kamata mu karfafa musu gwiwa da addu’a, su nuna jagoranci na gari domin moriyar al’umma."

A ranar Laraba ne dai aka yi faretin tuna wa da ranar 'yancin kan Najeriya, amma babu kwamishina ko jami'in 'dan sanda da ya halarci faretin.

Kwamishina ya fusata Gwamnan Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana bacin ransa kan rashin halartar bikin ƴancin kai da Kwashina da rundunar ƴan sanda ta yi.

A cewar gwamnan, hakan ba wai kawai cin mutuncinsa ba ne a matsayin babban jami’in tsaro na jihar, har ila yau cin mutunci ne ga daukacin al’ummar Kano a irin wannan lokaci.

Kara karanta wannan

Jerin tsofaffin gwamnonin Najeriya 7 da suka dawo manyan sarakuna

Gwamnan ya soki Kwamishinan ƴan sanda da nuna son kai da son zuciya, yana mai cewa rashin halartar rundunar ƴan sanda a bikin cikar Najeriya shekara 65 da 'yancin kai ya saba doka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng