Abba Ya Jero Bangarori 5 da Gwamnatin Kano Ta Farfado da Su a cikin Shekaru 2
- Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta taya 'yan Najeriya murnar cika shekaru 65 da samun 'yanci daga hannun Turawan mulkin mallaka
- Ya ce duk da gwamnatinsa ba ta jima ba, amma ta dauki hanyar farfado da bangarori daban-daban na ci gaban al'umma a shekaru biyu
- Daga bangaren ilimi kawai, Gwamna Abba ya ce ya dauki malamai 6,000 tare da saukaka kudin makaranta da tallafa wa dubunnan dalibai a Kano
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samu ci gaba mai tarin yawa a fannoni daban-daban duk da kalubalen tattalin arziki a Najeriya.
Abba ya bayyana haka ne a yayin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun 'yancin kai da aka gudanar a Filin wasa na Sani Abacha a jihar Kano.

Kara karanta wannan
Gwamna Uba Sani ya kinkimo aikin da aka kwashe shekara 50 ana alkawarin yi a Kaduna

Source: Facebook
A sakon da Darakta Janar na yada labaran Gwamnan, Sanusi Bature D-Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook, Abba ya jaddada kudurinsa na cika alkawuran da ya dauka a lokacin kamfen.
Daga cikin bangarorin da Gwamnan ya ce an samu ci gaba akwai:
1. Ilimi
A cikin sakon, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnati ta ware kusan 1/3 na kasafin kudin shekarar 2024 da 2025 ga harkar ilimi, lamarin da ya zarce ka’idar UNESCO.
Ya kara da cewa an dauki sababbin malamai 6,000 tare da ɗaukar masu aikin sa kai 2,000 a matsayin cikakkun ma’aikata a jihar.
Haka kuma, an rage kudin makaranta da 50% a manyan makarantu da gwamnati ke da su tare da biya wa dubunnan dalibai kudin jarrabawa.
2. Lafiya
A bangaren kiwon lafiya kuwa, Gwamna Abba ya ce Kano ta zarce ka’idar Abuja wajen ware kudi ga bangaren kiwon lafiya.

Kara karanta wannan
Kwamishinan 'yan sanda ya fusata Gwamna Abba a wurin faretin ranar 'yancin kai a Kano
Ya bayyana cewa an dauki karin ma'aikatan lafiya fiye da 500. Baya ga haka, an kafa Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC).
Daga cikin matakan saukaka wa mata a jihar, Gwamnan ya ce an kuma dan fara tiyata kyauta ga mata masu juna biyu.
3. Noma
A cewar Injiniya Abba Kabir Yusuf, gwamnatin ta raba takin zamani na ₦1bn ga manoma 52,800, tare da kaddamar da aikin ban ruwa na ₦16bn a madatsar ruwa ta Jakara.
Haka kuma, shirin KSADP ya tallafa wa manoma fiye da 477,000 — adadin da ya zarce yadda aka yi tsammani da fari.
3. Ababen more rayuwa
A bangaren ababen more rayuwa, Gwamnan ya ce an gyara tituna 17 a birnin Kano tare da ware ₦27bn don manyan ayyuka da suka hada da gadoji da hanyoyi.
Gwamna Abba ya kuma tabbatar da dawo da aikin bututun ruwa na Tamburawa da sayen karin injinan tura ruwa.
4. Kudin fansho
Gwamnatin ta kara da cewa ta fara biyan bashin fansho da ya kai ₦48bn, inda aka riga aka fitar da biliyan 27 zuwa yanzu.

Source: Facebook
Haka kuma ana biyan albashi da fansho a kan lokaci ba tare da an tara bashi ko an bar tsofaffin ma'aikata ba hakkinsu ba.
5. Mata da matasa
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta ƙaddamar da shirin kiwon dabbobi na biliyan 2.3, inda aka raba akalla awaki 7,158 ga mata 2,386 a faɗin kananan hukumomi 44.
Bugu da ƙari, an bai wa matasa 1,130 da suka kammala karatu kayan aiki don fara sana’a da dogaro da kansu, yayin da dubunnn ’yan ƙananan yan kasuwa suka jarin ₦50,000 kowanensu.
Gwamna Abba ya sha alwashin ci gaba da tafiya da gaskiya da rikon amana tare da tabbatar da ci gaban Kano mai ɗorewa.
Kwamishinan 'yan sanda ya fusata Gwamnan Kano
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya fito fili ya nuna rashin jin daɗinsa kan matakin da Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori.

Kara karanta wannan
Da sauran rina a kaba: Gwamna Abba ya yi maganar cikar Najeriya shekara 65 da 'yanci
Gwamna Abba ya zargi CP Bakori da nuna son zuciya bayan jami’an ‘yan sanda sun kauracewa biki da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha, Kano, a ranar Laraba.
An ji ya yi kira ga hukumomin tsaro a Najeriya da su ci gaba da yin aiki da gaskiya da rikon amana wajen kare martabar kasa, ba wai su zama 'yan amshin shatan wasu ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
