Sokoto, Kebbi da Jihohin Arewa 5 za Su Fuskanci Ambaliya, Gwamnati Ta Yi Gargadi
- Gwamnatin tarayya ta sake yin gargadi kan ambaliyar ruwa a jihohi bakwai na Arewacin Najeriya daga 1 zuwa 3 ga Oktoba 2025
- Jihohin da ke cikin hadari sun hada da Adamawa, Kebbi, Bauchi, Zamfara, Sokoto, Kaduna da Neja, inda Kebbi ta fi fuskantar barazana
- NEMA ta ce ambaliya ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 232 a Najeriya a Satumba, ta kuma tilasta wa fiye da 121,000 barin gidajensu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya ta sake yin gargadi game da yiwuwar ambaliyar ruwa mai muni a wasu jihohin Arewacin Najeriya bakwai.
Wannan karin gargadin, ya biyo bayan gargadin ambaliyar da ma'aikatar muhalli ta tarayya, ta bakin FEW da ta fitar a karshen Satumba, 2025.

Source: Getty Images
Ambaliya za ta shafi jihohin Arewa 7
Daraktan sashen zaizayar kasa, ambaliya da yankunan bakin teku na ma'aikatar muhalli ta tarayya, Usman Abdullahi Bakani ya sanar da hakan, inji rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, Usman Bokani ya yi nuni da cewa wadannan jihohi bakwai za su fuskanci ruwa mai yawa da zai jawo ambliya daga 1 zuwa 3 ga Oktoba, 2025.
Jihohin da da aka sanya a sabon hasashen ambaliyar sun hada da Adamawa, Kebbi, Bauchi, Zamfara, Sokoto da kuma Kaduna da Niger.
Kebbi ce sanarwar ta ce take da munin hadarin ambaliya, domin ambaliyar za ta shafi garuruwan Argungu, Bagudu, Ganri-Banza, Gwandu, Jega, Kalgo, Kamba, Kangiwa da Birnin Kebbi.
Gwamnati ta gargadi yankunan Arewa
Jihar da ambaliyar ba za ta yi wa barna sosai ba ita ce Kaduna, inda ake hasashen ambaliyar za ta shafi Jaji da Zaria kawai. Sai kuma jihar Neja, wacce Magama da Sarkin-Pawa ke cikin hadarin ambaliya.
Wasu manyan garuruwan Arewa da ambaliyar za ta shafa sun hada da Mubi, Argungu, Birnin Kebbi, Sokoto, Gusau, Azare da kuma Jega.
Usman Bokani ya bukaci masu ruwa da tsaki da wakilan gwamnatin jihohi da ke a dandalin cibiyar FEW da su rika ba da rahoton halin da yankunansu ke ciki.
Ya kara ba jama'a shawarar cewa su guji zama a garuruwan da ke bakin teku ko wata babbar hanyar ruwa, sannan a kwashe mutane daga yankunan da ke fuskantar ambaliyar.

Source: Twitter
'Ambaliya ta hallaka mutane 232' - NEMA
Wannan gargadin dai na daga cikin gargadin lokaci-zuwa-lokaci da ma'aikatar muhalli ke fitarwa game da ambaliya don kare rayuka da dukiyoyin jama'a.
Ambaliyar ruwa na ci gaba da zama mafi munin masifa a Najeriya, wacce ta daidaita dubunnan mutane, ta lalata kadarori da jawo karancin abinci, inji rahoton Punch.
A cewar hukumar ba da agajin aggawa ta kasa (NEMA), fiye da mutane 232 ne suka mutu, yayin da wasu 121, 224 suka rasa muhallansu biyo bayan ambaliya da ta mamaye sassan kasar nan a ranar 20 ga Satumba, 2025.
Rahoton NEMA ya nuna cewa akalla mutane 339,658 ne ambaliyar ruwa ta shafa, kuma akalla mutum 681 suka jikkata daga wannan iftila'i.
Ambaliya ta cinye gidaje a jihohin Arewa 3
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ruwan sama mai yawa ya jawo rushewar gidaje da cinye gonaki a jihohin Bauchi, Filato da Neja.
A Filato, sama da gidaje 50 da makarantu da majami’a sun rushe yayin da guguwar ta kakkarya bishiyoyi, ta fasa turakun wuta.
A Bauchi da Neja, ambaliya ta cinye gonaki da dama, inda hukumar SEMA ta sanar da shirin fara kai tallafi ga wadanda abin ya shafa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


