Bayan Shafe Shekaru Yana Koyar da Alkur'ani a Masallacin Annabi SAW, Sheikh Bashir Ya Rasu
- Sheikh Bashir bin Ahmed Siddiq, malamin da ke koyar da Alkur'ani a masallacin Annabi S.A.W a Madina ya riga mu gidan gaskiya
- Hukumomin kasar Saudiyya sun tabbatar da rasuwar babban malamin, wanda ya shafe sama da shekaru 60 yana koyar wa a masallacin Annabi
- A sanarwar da Saudiyya ta fitar, ta ce Sheikh Bashir ya shafe kusan duka rayuwarsa wajen koyar da Alkur'ani Mai Girma a Madina
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Madina, Saudi Arabia - Musulmi sun yi babban rashi da aka tabbatar da rasuwar daya daga cikin manyan malaman da ke koyar da Alkur'ani a masallacin Annabi SAW da ke Madina.
Rahotanni daga kasar Saudiyya sun tabbatar da cewa Sheikh Bashir bin Ahmed Siddiq, ya riga mu gidan gaskiya a yau Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da hukumar kula da manyan masallatai biyu masu alfarma da ke Makkah da Madina ta wallafa a shafinta Inside The Haramain na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Bashir bin Ahmed ya rasu a Madina
Sheikh Bashir na ɗaya daga cikin manyan malamai masu koyar da Alƙur’ani Mai Girma da karatunsa a Masallacin Manzon Allah (SAW) da ke birnin Madina.
Sanarwar ta ce:
"InnalilLahi wa inna ilaihi raji'un, daya daga cikin manyan malamai masu koyar da Alƙur’ani Mai Girma da karatunsa a Masallacin Manzon Allah (SAW) a Madina, Sheikh Bashir bin Ahmed Siddiq, ya rasu a yau Laraba."
Sheikh Bashir ya sadaukar da kusan shekaru 60 na rayuwarsa wajen koyar da Alƙur’ani a Masallacin Annabi, inda dubban ɗalibai suka yi karatu a ƙarƙashinsa.
Manyan malaman da Sheikh Bashir ya koyar
Daga cikin fitattun ɗaliban da marigayin ya koyar akwai:
- Sheikh Muhammad Ayyoub da Sheikh Ali Jaber – tsofaffin limaman manyan masallatar biyu masu alfarma (Allah ya jikansu da rahama).
- Sheikh Muhammad Al-Mukhtar Al-Shanqiti – mamba a Majalisar Manyan Malamai ta kasar Saudiyya.
- Sheikh Abdul Muhsin Al-Qasim da Sheikh Salah Al-Budair – limaman yanzu na Masallacin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad SAW da ke Madina.

Kara karanta wannan
'Yan Boko Haram sun yi ta'addanci a Borno, an kona fadar basarake, an kashe mutane
Marigayi Sheikh Bashir ya kasance mutum mai tawali'u, wanda ake daukarsa a matsayin ginshiƙi wajen ilimin Alƙur’ani a Masallacin Annabi.

Source: Facebook
Shehin Malamin ya bar gadon ilimi da ɗalibai da ke ci gaba da hidimar Alƙur’ani a fadin duniya ta Musulunci.
"Allah Maɗaukaki Ya ji kansa, Ya karɓi kyawawan ayyukanda hidimarsa ga Alƙur’ani Mai Girma ta tsawon shekaru, ya kuma ɗaukaka matsayinsa tare da salihan bayi," in ji sanarwar.
Babban Mufti na Saudiyya ya kwanta dama
A wani labarin, kun ji cewa Saudiyya ta sanar da rasuwar babban mufti na ƙasar, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah Al Sheikh, yana da shekara 82 a duniya.
Kafin rasuwarsa, Sheikh Al Sheikh ya rike mukaman da suka haɗa da babban mufti na Saudiyya, shugaban Majalisar Manyan Malamai, da kuma shugaban hukumar bincike da bayar da fatawa.
Sarki Salman da Yarima Mohammed bin Salman sun mika ta’aziyarsu ga iyalan marigayin, al’ummar Saudiyya da kuma musulmin duniya baki ɗaya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
