PDP Ta Rusa Dukkanin Shugabanninta a Jihohi 2, Ta Nada Kwamitocin Riko
- Jam’iyyar PDP ta rusa shugabanninta a jihohin Akwa Ibom da Cross River, tare da kafa kwamitocin rikon kwarya na wata uku
- A Akwa Ibom, rushewar shugabannin PDP ya biyo bayan sauya sheƙar Gwamna Umo Eno zuwa APC da rikicin shugabanci na jam’iyya
- A Cross River, PDP ta nada Bassey Eko Ewa matsayin shugaban rikon kwarya bayan karewar wa’adin shugabannin jihar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya, PDP, ta rusa shugabancin jam’iyyar a jihohin Akwa Ibom da Cross River.
Bayan rushe shugabanci a jihohin biyu, PDP ta kuma kafa sababbin kwamitocin riko da za su jagoranci harkokin jam’iyyar na wucin gadi.

Source: Twitter
An bayyana matakin ne a wata sanarwa da kakakin jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba, ya wallafa a shafin PDP na X a ranar Talata, 30 ga Satumba, 2025.
Debo Ologunagba ya bayyana cewa kwamitin NWC na PDP ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya ba shi wajen rusa shugabancin jam’iyyar a Akwa Ibom.
Rikicin PDP a jihar Akwa Ibom
PDP ta kasance jam’iyya mai mulki a Akwa Ibom sama da shekaru 20, sai dai ta rasa wannan matsayi a watan Yuni, 2025 bayan da Gwamna Umo Eno ya sauya sheka zuwa APC.
Duk da haka, Eno ya nace cewa zai ci gaba da riƙe ikon shugabancin PDP a jihar, lamarin da ya haifar da 'yan guna-guni a jam'iyyar.
Tsohon shugaban jam’iyyar a jihar, Aniekan Akpan, ya sha bayyana biyayyarsa ga Eno, duk da sauya shekar gwamnan zuwa APC, abin da ya jawo aka nemi ya yi murabus.
Yanzu da kwamitin NWC na PDP ya rusa shugabancin jam’iyyar a jihar, Gwamna Eno ya rasa ikon da yake da shi akan tsarin jam'iyyar a Akwa Ibom.
Sababbin shugabannin da aka nada sun hada da waɗanda suka sha sukar gwamnan, ciki har da Unwana Assam.
Mr. Ologunagba ya bayyana cewa Igwa Umoren zai shugabanci kwamitin rikon jam’iyyar a Akwa Ibom, tare da Borono Bassey a matsayin sakataren kwamitin.
Kwamitin zai yi aiki na tsawon watanni uku kacal ko har zuwa lokacin da aka gudanar da sabon zaɓe na shugabannin jiha.

Source: Twitter
Rigimar da PDP ke fama da ita a Cross River
Haka zalika, PDP ta sanar da kafa kwamitin riko a jihar Cross River, bayan karewar wa’adin shugabannin jiha da aka zaɓa shekaru hudu da suka gabata.
Kwamitin zai fara aiki daga Laraba, 1 ga Oktoba, 2025, na tsawon watanni uku ko har zuwa lokacin da aka gudanar da sabon zaɓen shugabannin jiha.
Rt. Hon. Bassey Eko Ewa aka nada a matsayin shugaban kwamitin, yayin da Dr. Bassey Joseph Adim zai zama sakataren kwamitin, kamar yadda sanarwar PDP a X ta nuna.
Jam’iyyar PDP ta bukaci shugabanni, masu ruwa da tsaki da mambobinta a jihohin biyu da su ci gaba da zama tsintsiya madaurinki ɗaya domin tabbatar da cigaban jam’iyyar.
Ana fargabar gwamna zai bar PDP zuwa APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kusoshin PDP sun fara nuna damuwarsu kan jita-jitar da ke nuna Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu zai koma APC.
Tsohon shugaban PDP a Enugu, Cif Augustine Nnamani, ya zargi jam'iyyar da kokarin korar Gwamna Peter Mbah, yana mai cewa ita ce ke da laifi.
Ya kuma tabbatar da cewa Gwamna Mbah na ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin yanke hukuncin karshe kan yiwuwar barin PDP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


