Hatsarin Jirgi Ya Rutsa da 'Yan Kasuwa bayan Sun Baro Gida, An Rasa Rayuka
- Hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da yan kasuwan da suka fito daga yankin karamar hukumar Ibaji ta jihar Kogi zuwa kasuwar Ilushi
- Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce akalla mutane 26 ne suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin
- Gwamna Ahmed Ododo ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan mamatan tare da tabbatar masu cewa gwamnati za ta taimaka masu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Wani jirgin ruwa da ya dauko 'yan kasuwa ya gamu da hatsari mai muni a jihar Kogi, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane akalla 26.
Gwamnatin Kogi ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta yi alhinin rasuwar mutanen da hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a Kogin Neja.

Source: Facebook
Jirgin ruwa ya yi hatsari a jihar Kogi
Rahotan Channels tv ya nuna cewa jirgin ruwan ya dauko ’yan kasuwar da suka fito daga karamar hukumar Ibaji ta jihar Kogi da nufin zuwa kasuwar Ilushi da ke jihar Edo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai suna cikin tafiya a cikin Kogin Neja wanda ya ratsa ta cikin jihar Kogi kwatsam jirgin ruwan ya nutse da yammacin Talata, 30 ga Satumba, 2025.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa yawan mutanen da suka mutu a hatsarin ya karu zuwa 26.
“Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan mummunan lamari ya yi ajalin aƙalla fasinjoji 26. Wannan babban rashi ne mai tayar da hankali.
"Zuciyarmu da addu’o’inmu su na tare da iyalan wadanda abin ya shafa, da kuma daukacin al’ummar Ibaji a wannan lokacin na bakin ciki,” in ji sanarwar.
Gwamna Ododo ya yi jimamin hatsarin jirgin
Hon. Fanwo ya ce mai girma gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo, ya aike da ta’aziyya ga iyalan wadanda da suka rasu, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
Ya kuma umarci hukumomin da abin ya shafa, ciki har da hukumar agaji ta SEMA, da su yi aiki don bada taimakon gaggawa ga wadanda lamarin ya rutsa da su.

Kara karanta wannan
'Yan Boko Haram sun yi ta'addanci a Borno, an kona fadar basarake, an kashe mutane
Gwamna Ododo ya kara tabbatar da cewa gwamnatin jihar Kogi za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da hukumomin tarayya don inganta tsaro a hanyoyin ruwa, domin kauce wa irin haka nan gaba.

Source: Getty Images
Gwamnatin Kogi ta ja hankalin jama'a
Ya kuma yi kira ga jama'a, musamman mazauna yankunan ruwa, da su rika bin ka'idoji kamar kauce wa ɗora kaya a jirgin ruwa fiye kima da sanya rigar ruwa.
“Gwamnatin jihar Kogi na tare da mutanen karamar hukumar Ibaji, kuma za ta ci gaba da tallafa musu a wannan mawuyacin lokaci,” in ji gwamnan.
Jirgin ruwa ya yi hatsari a Sakkwato
A wani labarin, kun ji cewa jirgin ruwa da ya dauko mutanen da suka gudu daga harin yan bindiga ya nutse a yankin karamar hukumar Sabon Birni a Sakkwato.
Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa jirgin, wanda ya dauko mata da yara ya yi hatsari ne sakamakon bugun bakin gada ranar Alhamis.
Wani mazaunin garin, Zayyanu Zalla Bango ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin Legit Hausa, ya ce an tabbatar da mutuwar mutum tara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
