An Hallaka Shedanin Dan Bindiga, Matasa Sun Kona Fadar Sarki da Harsashi Ya Samu Dalibai
- Sojojin Operation Whirl Stroke sun yi nasara kan wani kasurgumin dan ta'adda wanda ya sheka barzahu yayin arangama
- Dakarun sojojin sun kashe ɗan fashi a Jato-Aka, amma harbin bazata ya rutsa da ɗalibai uku, ɗaya mace wacce ta rasu
- Lamarin ya tayar da zanga-zanga a garin Jato-Aka, matasa sun fito tituna suka ƙone ofishin mai sarautar gargajiya, Mue Ter
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue – Sojojin Operation Whirl Stroke sun kashe wani da ake zargin ɗan bindiga ne a lokacin artabu da suka yi.
Lamarin ya faru ne a Jato-Aka, ƙaramar hukumar Kwande a jihar Benue a ranar Talata 30 ga watan Satumbar 2025.

Source: Facebook
Shedanin dan bindiga ya bakunci lahira
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa harbin ya wuce inda ya rutsa da ɗalibai uku, inda ɗaya daga cikinsu ta rasa ranta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:20 na rana, lokacin da sojojin ke sintiri a yankin.
An ce rikicin ya fara ne bayan da suka hango wasu da ake zargi ’yan bindiga ne a kan babur suna ɗauke da makamai.
A cewar wani shaidar gani da ido, ’yan bindigar ne suka fara bude wuta bayan ganin sojojin.
Sojojin sun mayar da martani, inda aka harbe ɗaya daga cikin su har lahira, sauran kuma suka tsere suka bar baburansu.
Dalibar makaranta ta mutu bayan harbin bindiga
Sai dai a lokacin, wasu ɗaliban makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati da ke Jato-Aka da suke dawowa, sun ci karo da harbin ba tsammani.
Wata ɗaliba mace daga cikinsu daga baya an tabbatar da mutuwarta a asibitin NKST, yayin da sauran biyun ke karɓar magani.
Rundunar sojoji ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa sojojin kawai sun kare kansu ne bayan an bude musu wuta.

Source: Original
Matakin da matasa suka dauka a Benue
Rahotanni sun nuna cewa labarin rasuwar ɗalibar ya tayar da tarzoma a garin Jato-Aka, inda fusatattun matasa suka yi zanga-zanga tare da ƙone ofishin mai sarautar gargajiya na yankin, Mue Ter.
Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin, tana mai cewa an jibge jami’an yan sanda a garin don dawo da zaman lafiya.
Ta kara da cewa an kwantar da tarzoma, sai dai ana ci gaba da sintiri don hana sake tashin rikici.
Hukumomi sun roki al’ummar Jato-Aka da su kwantar da hankali su kuma yi aiki tare da jami’an tsaro yayin da ake ci gaba da bincike.
An kashe dan bindiga bayan ya tuba
Mun ba ku labarin cewa an kama mutum daya bisa zargin hannu a kisan wani tsohon dan bindiga da ya tuba a yankin Zaki-Biam, jihar Benue.
Rahotanni sun ce tsohon dan bindigan ya rasa ransa ne bayan wasu mutane sun bi shi a babur sun harbe shi ba tare da bata lokaci ba.
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa tana ci gaba da bincike domin kama sauran wadanda suka gudu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


