PEGASSAN vs Dangote: An Rufe Gidajen Mai, an Samu Raguwar Karfin Wutar Lantarki
- Yajin aikin PENGASSAN ya tilasta rufe gidajen mai da dama a fadin Najeriya, lamarin da ya jawo karancin mai da dogayen layuka
- An rahoto cewa farashin mai da 'yan bunburutu ke sayarwa a bayan fage ya kai tsakanin N1,350 da N1,500 a kan kowace lita
- Ba iya karancin man fetur yajin aikin ya jawo ba, an ce an samu saukar wutar lantarki da ake rarrabawa kamfanonin DisCos a kasar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - A ranar Talata, 30 ga Satumba, aka rufe wasu gidajen mai a sassan Najeriya, yayin da yajin aikin da ƙungiyar PENGASSAN ta ayyana ya shiga rana ta biyu.
Wannan ya tilasta masu abubuwan hawa bin dogayen layukan neman mai, yayin da masu sayarwa a bunburutu suka fara mamaye a manyan birane.

Source: UGC
Tasirin yajin aikin kungiyar PENGASSAN
Binciken da aka gudanar a cikin Abuja da kewaye ya nuna cewa yawancin gidajen mai sun bi umarnin ƙungiyar wajen daina sayar da mai, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yajin aikin ya kuma tsayar da ayyuka a wasu muhimman hukumomin gwamnati a bangaren man fetur, ciki har da NNPC Ltd., NUPRC, da NMDPRA.
Duk da cewa matatar Dangote mai darajar dala biliyan 20 ta ci gaba da lodi da rarraba mai ga abokan hulɗa a ranar Litinin da Talata, yawancin tankokin dakon mai da kuma gidajen mai sun dakatar da aiki domin bin umarnin PENGASSAN.
'Yan bunburutu na sayar da fetur da tsada
Wannan ya jefa tsoro a zukatan mutane, inda masu ababen hawa suka yi tururuwa zuwa gidajen man da aka ci sa'a suka buɗe.
An rahoto cewa, an ga dogayen layukan neman mai sun dawo a Abuja da Legas a ranar Talata, kafin sanarwar kungiyar na janye yajin aiki.

Kara karanta wannan
Bayan soke fareti, Tinubu ya fadi abin da ya faru da shi a daren 1 ga Oktoba 2025
Karancin man fetur ya jawo masu ababen hawa sun koma sayen mai a wajen 'yan bunburutu, inda jarka mai cin lita 10 ta kai N13,500 zuwa N15,000, watau N1,350 zuwa N1,500 a kan kowace lita, fiye da ninki biyu kan farashin N900 na gwamnati.

Source: Getty Images
Wutar lantarki ta fadi kasa da 3,500MW
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa matsalar yajin aikin ta bazu zuwa bangaren wuta, inda samar da lantarki ya fadi zuwa 3,500MW a safiyar Talata.
Bayanai daga tushen wutar sun nuna cewa wutar da aka raba wa kamfanonin DisCos ta ragu zuwa 3,656MW da misalin ƙarfe 6:00 na safiya, inda Abuja DisCo ta samu 509MW, Ikeja Electric 502MW, da Eko DisCo 427MW.
Yawancin tashoshin wutar gas sun daina aiki, sai dai Delta (404MW) da Odukpani NIPP (209MW) suka rage a kan layi.
Hukumar NISO ta danganta wannan matsala da yajin aikin PENGASSAN, inda ta ce samar da wuta ya fadi daga 4,300MW a ranar Lahadi, 28 ga Satumba, zuwa 3,200MW.
A zantawarmu da Alhaji Babangida Tsohon Kudi, ya ce duk abin da ke faruwa, yana faruwa ne saboda son zuciyar wasu, da kuma son lallai sai sun samu biyan bukatunsu.
"Ni a mahangata, abin da kungiyar PENGASSAN take yi ba dai dai ba ne. Bawan Allahn nan shi kadai ya san fadi tashin da ya yi ya gina matatar nan, rana daya wani ba zai zo ya ce zai juya akalar ma'aikatansa ba.
"Idan fa ana son zaman lafiya ne, to lallai a zauna a tattauna, a cimma matsaya mai yiwuwa, don akwai bukatun da kungiyar ta gabatar da hankali ba zai dauka ba.
"Ni fa ban ga laifin Dangote ba, dole ne ya yi duk mai yiwuwa don kare matatar nan, ya kashe makudan kudi, ba zai yarda wasu tsiraru su hana shi rawar gaban hantsi ba."
- Alhaji Babangida Tsohon Kudi.
Hassan Rano kuwa, ya roki kungiyar PENGASSAN da ta sakarwa Dangote mara ya ji dadin fitsari, yana mai cewa, farashin fetur ya fara sauka saboda Dangote.
"Wallahi mu nan har mun fara murna, fetur ya fara sauka, an fara samun sauki, to gashi kuma ana so a jawo mu koma 'yar gidan jiya.
"Don Allah gwamnati ta shiga tsakanin Dangote da kungiyoyin nan, a bar shi mu dai mu samu saukin fetur, ko ma samu saukin kayan masarufi."
- Hassan Rano.
Gwamnati ta shiga tsakanin Dangote, PENGASSAN
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta shawo kan rikicin kungiyar PENGASSAN da Matatar man Dangote.
PENGASSAN da kamfanin Dangote sun cimma wata matsaya tare da kulla yarjejeniya a zaman shiga tsakani da gwamnati ta yi.
Daga cikinsu yarjejeniyon, kungiyar PENGASSAN ta hakura, za kuma ta janye yajin aikin da ta tsunduma, wanda ake sa ran zai iya gurgunta kasar nan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


