Ikon Allah: An Haife Jariri Mai Fuska 2, Ido 4 a Jihar Bauchi

Ikon Allah: An Haife Jariri Mai Fuska 2, Ido 4 a Jihar Bauchi

  • Wata mata a Bauchi ta haifi jariri mai fuska biyu da kai guda, abin da ya dauki hankalin al'umma saboda ganin wani bakon al'amari
  • An yi wa matar mai suna Hannatu tiyata kyauta a babban asibitin Azare, inda likitoci suka tabbatar da cewa wannan jariri yana da bakin siffofi
  • Iyayen jaririn sun roki gwamnati da al'umma da su tallafa musu saboda rashin hali da bukatar kulawa ta musamman da yaron zai bukata

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi – A wani lamari mai cike da al'ajabi, wata mata mai suna Hannatu, da ke zaune a kauyen Magonshi, ta haifi jariri mai fuska biyu da kai guda daya.

Allah Ya sauke ta lafiya lau a babban asibitin gwamnatin jihar Bauchi da ke Azare, inda likitoci su ka ce ba kasafai ake ganin irin wannan haihuwa ba.

Kara karanta wannan

Da sauran rina a kaba: Gwamna Abba ya yi maganar cikar Najeriya shekara 65 da 'yanci

An haifi jariri mai halittar al'ajabi a Bauchi
Jaririn da aka haifa mai siffar ban mamaki a Bauchi Hoto: Ibrahim Sweetor/Murtala Hamza Tsafe
Source: Facebook

A hira da Mijin Hannatu, Malam Bala Sa’idu, ya yi da jaridar Aminiya, ya bayyana cewa lamarin wani mu’ujiza ne daga Allah SWT.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bauchi: Abin da iyayen jaririn ke cewa

Malam Bala Sa’idu, ya ce duk da cewa jaririn bai zo da kamanni na yau da kullum ba da aka saba gani ba, sun karɓi lamarin da hannu biyu da yardar Allah.

A cewarsa, matarsa ta ranini cikin har na tsawon makonni 42, wanda ya zarce lokacin haihuwa na al’ada da jama'a su ka sani.

Ya gode wa babban likitan asibitin, Dr. Bello Idris, wanda ya jagoranci tiyatar haihuwar ba tare da karɓar ko sisin kwabo ba.

Malam Bala ya roki gwamnatin jihar Bauchi da kungiyoyin agaji su taimaka masu ganin an ceto lafiyar jaririn, kasancewar su ba su da halin biyan kuɗin kula da lafiyarsa a gaba.

Likitocin Bauchi sun yi mamaki

Dr. Bello Idris, babban likitan da ya jagoranci tiyatar, ya bayyana cewa a duk tsawon shekarunsa a aikin likitanci, bai taba ganin irin wannan yanayi ba.

Kara karanta wannan

Rasha ta kai sabon hari Gabashin Turai, ta harba makamai masu linzami a Ukraine

Ya ce irin wannan jariri yana faruwa ne sau daya cikin mutum miliyan 10, kuma sun jinjina al'amarin sosai.

Iyayen jaririn Bauchi sun nemi daukin gwamnati
Hoton Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed Hoto: Senator Bala Mohammed
Source: Facebook

Dr. Bello Idris, ce jaririn na da kai daya, fuska biyu, idanu hudu, hanci biyu, baki biyu, kunne biyu, hannaye biyu da ƙafafu biyu.

Sai dai duka baki biyu da ya ke da su sun zo a tsage, saboda haka ana shan wahala wajen shayar da shi yadda ya kamata.

Dr. Idris ya bayyana cewa bayan mahaifiyar ta samu sauki, za a tura su zuwa Babban Asibitin Koyarwa na Tarayya (FUHSTA) da ke Azare domin ci gaba da duba lafiyar jaririn da gudanar da bincike kan yanayinsa.

Uba ya kashe dansa a jihar Bauchi

A baya, mun wallafa cewa rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wani mutum mai suna Musa Bala kan zargin kashe jaririnsa dan kwanaki biyar da haihuwa.

Kakakin hukumar ‘yan sanda, DSP Kamal Datti Abubakar, ya bayyana cewa an kama su ne bisa zargin su biyu sun yi tarayya wajen ɗura wa jaririn maganin kwari mai guba.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Yadda 'Dan sanda ya harbe kansa har lahira a Kano

Rundunar ta tabbatar da cewa za a tuhumi mutanen biyu da laifin kisan kai, lamarin da ya kara jefa jama'a d ake zaune a yankin da sauran makwabta a cikin mawuyacin hali.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng