Wani mahaifi ya kashe jaririnsa ɗan kwanaki biyar da haihuwa a jihar Bauchi

Wani mahaifi ya kashe jaririnsa ɗan kwanaki biyar da haihuwa a jihar Bauchi

Hukumar 'yan sanda ta jihar Bauchi, ta cafke wani mahaifi Musa Bala, da laifin kisan jaririnsa ɗan kwanaki biyar da haihuwa.

Wannan mahaifi ya shiga hannu ne tare da wani abokin sa suka aikata laifin tare kamar yadda kakakin hukumar 'yan sandan jihar ya bayyanar.

DSP Kamal Datti Abubakar ya bayyana cewa, wannan mutane biyu sun yi tarayya wajen ɗurawa jaririn shahararren maganin kwari na piya-piya.

Wani mahaifi ya kashe jaririnsa ɗan kwanaki biyar da haihuwa a jihar Bauchi
Wani mahaifi ya kashe jaririnsa ɗan kwanaki biyar da haihuwa a jihar Bauchi
Asali: Depositphotos

Wani saurayi, Nuhu Bulus ɗan shekara 17 a duniya, ya shiga hannun hukumar da laifin kisan mahaifinsa, Bulus Gazi na gundumar Boloji a karamar hukumar Toro ta jihar.

KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya za ta baiwa 'yan Najeriya 8m kulawar lafiya kyauta a 2018

A cewar hukumar 'yan sandan, saurayin ya yi amfani da makamai daban-daban wajen sheme mahaifin na sa, inda ya ce ga garin ku nan a babban asibitin garin Toro.

A yayin haka dai, hukumar ta kuma cafke wasu 'yan ta'adda masu fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng