Tinubu Ya Sake Magana kan Cire Tallafi, Ya Fadi Abin da 'Yan Najeriya ba Su Sani ba
- Har zuwa yanzu Shugaba Bola Tinubu na ci gaba da magana game da cire tallafin mai da ya jawo wahalhalu ga yan Najeriya
- Tinubu ya ce cire tallafin mai ba abu ne mai sauki ba, amma wajibi ne domin ceto tattalin arzikin Najeriya daga durkushewa
- Shugaban ya bayyana cewa kudin da aka samu daga cire tallafin ana karkatar da su zuwa ilimi, lafiya, tsaro, noma da ayyukan more rayuwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake magan kan cire tallafin mai da ake ganin shi ne sanadin wahalhalu a Najeriya.
Tinubu ya ce matakin da gwamnatinsa ta dauka na cire tallafin man fetur ba mai sauki ba ne, amma wajibi ne don ceto tattalin arzikin kasar.

Source: Facebook
Tinubu ya magantu kan cire tallafin mai
Hakan na cikin jawabin da shugaban ya yi game da bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun 'yanci wanda Bayo Onanuga ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya tabbatar da cewa cire tallafin mai din ba abin ba ne mai sauki inda ya ce ya ceto kasar daga rugujewa da kuma mayar da arzikin kasa ga jama’a.
Shugaban ya bayyana cewa ya gaji tattalin arzikin da ya kusa durkushewa, don haka dole ne a dauki tsauraran matakai.
Ya ce gwamnati ta zabi hanyar sauyi domin kare makomar kasa fiye da jin dadin wucin gadi.
Shugaban ya bayyana cewa tsarin tallafi da musayar kudi daban-daban ya bai wa ’yan tsiraru damar cin moriyar arzikin kasa, yayin da mafiya yawan jama’a ba su amfana da komai.

Source: Facebook
Amfanin cire tallafin mai ga Najeriya
Tinubu ya jaddada cewa kudaden da aka samu daga cire tallafin mai yanzu ana karkatar da su zuwa fannin ilimi, lafiya, tsaro.
Ya tabbatar da cewa an samu ci gaba a bangaren noma da ayyukan more rayuwa, domin inganta rayuwar talakawa.
Shugaban ya kuma amince cewa sauye-sauyen sun jawo wahalhalu a tsakanin al’umma, amma ya ce wannan sadaukarwa tana kawo riba a hankali, domin guje wa fadawa cikin bala’in tattalin arziki ko karyewar kasa.
Ana iya tuna cewa a ranar 29 ga Mayu 2023, Tinubu ya bayyana a hukumance cewa “ya cire tallafin mai”, wanda nan take ya jawo tsadar mai da tashin farashin kayayyaki a fadin Najeriya.
Wannan mataki ya jefa al'ummar Najeriya cikin kunci wanda ku san har yanzu ba su farfado ba duk da cewa farashin kayan abinci ya dan sauka fiye da bara.
Tinubu ya kadu bayan kisan yar jarida a Abuja
Kun samu labarin cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa wata fitacciyar yar jarida a birnin tarayya, Abuja.
Tinubu ya jajanta wa iyalan marigayiya Somtochukwu Maduagwu, mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin Arise News wacce ta rasa ranta bayan harin yan fashi a gidanta.
Shugaban ya umurci jami’an tsaro da su gudanar da bincike cikin gaggawa don kamo wadanda suka aikata wannan mummunan aiki kan matashiyar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

