Nigeria @65: Atiku Ya Caccaki Tinubu kan Yunwa da Tsaro, Ya Bukaci Kifar da APC

Nigeria @65: Atiku Ya Caccaki Tinubu kan Yunwa da Tsaro, Ya Bukaci Kifar da APC

  • Atiku Abubakar ya ce gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gaza kula da samar da jin daɗi da tsaron ’yan Najeriya
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya ce yunwa da kashe-kashe sun addabi al’umma, amma gwamnati ba ta damu ba
  • Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su yi amfani da ƙuri’unsu wajen kawar da gwamnatin da ba ta cika alkawari ba a zabe mai zuwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar suka ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Rahotanni sun nuna cewa Atiku Abubakar ya zargi gwamnati da sakaci wajen kare rayuka da jin daɗin ’yan Najeriya.

Atiku tare da shugaba Bola Tinubu
Atiku tare da shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga|Atiku Abubakar
Source: Getty Images

Legit ta tattaro bayanan da mataimakin shugaban kasar ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Nigeria @65: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu ya fada a jawabin ranar samun 'yanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya soki Tinubu a ranar murnar 'yanci

Yayin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yanci, Atiku ya ce duk da arzikin albarkatu da Najeriya ke da shi, mutane da dama sun koma ’yan gudun hijira da masu bara a ƙasarsu.

A cewar sa, yunwa da kashe-kashe na addabar jama’a a sassa daban-daban na ƙasar, yayin da shugabanni ke ci gaba da zama ba tare da ɗaukar matakin da ya dace ba.

Punch ta wallafa cewa ya kara da cewa gwamnatin Tinubu ta gaza, lamarin da ya jefa miliyoyin ’yan ƙasa cikin kunci da halin baƙin ciki.

Atiku ya ce abin takaici ne ƙasa mai yalwar albarkatu ta koma matsuguni ga talauci da rashin tsaro, inda wasu ke mutuwa da yunwa yayin da wasu ke rasa rayukansu sakamakon hare-hare.

Kiran Atiku kan kifar da Bola Tinubu

Atiku Abubakar ya jaddada cewa dimokuraɗiyya na bai wa jama’a damar sauya gwamnati ta hanyar ƙuri’a.

Kara karanta wannan

Taron tsintsiya: Fadar Shugaban Kasa ta fadi kallon da Tinubu ke yi wa 'yan hadaka

Ya ce duk da tsananin azaba da al’umma ke ciki a yau, zaɓe ne kawai mafita ga kawar da gwamnatin da ya kira maras tasiri.

Ya kara da cewa babu wata ƙungiya ko tafiyar siyasa da za ta iya kwace ikon zaɓe daga hannun jama’a idan suka tashi tsaye wajen kare muradunsu a zaɓen da ke tafe.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. Hoto: Paul O. Ibe
Source: Facebook

Atiku: Najeriya na tafiyar hawainiya

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa Najeriya ta cika shekaru 65 a matsayin ƙasa mai 'yanci, amma tana tafiyar hawainiya saboda shugabanci maras nagarta da cin hanci.

Ya ce wannan tarihi ya samo asali ne daga dogon lokaci na gurguntar da ƙasa ta hanyar halaye marasa kyau a shugabanci.

Sai dai Atiku ya ce har yanzu ana fata shugabanci mai inganci zai iya ɗaga Najeriya daga cikin ruɓaɓɓen tsarin da take ciki zuwa matakin da ya dace a idon duniya.

Duk da suka da tsawatarwarsa, Atiku Abubakar ya yi fatan alheri ga ’yan Najeriya a wannan rana ta samun ’yancin kai.

Maganar Shugaba Tinubu a ranar yanci

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ta tsallake mawuyacin yanayi.

Kara karanta wannan

Nigeria @65: Jawabin da Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya a yau 1 ga Oktoba 2025

A cikin jawabinsa na 1 ga Oktoba, 2025, Tinubu ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakai masu wahala amma masu amfani.

Shugaban ya lissafa nasarorin da ya samu kamar cire tallafin man fetur domin farfado da tattali da yai da rashawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng