"A Fito da Rahoto": Otedola Ya Fusata kan Zarginsa da Badakalar Tallafin Mai

"A Fito da Rahoto": Otedola Ya Fusata kan Zarginsa da Badakalar Tallafin Mai

  • Hamshakin ɗan kasuwa, Femi Otedola, ya ce an fara yunƙurin bata masa suna ta hanyar tsoma shi a cikin batun tallafin man fetur
  • A wani sako da ya fitar, ya ce ya lura da yadda hadimin tsohon mataimakin Shugaban Kasa, Umar Sani na fadin karya a kansa
  • Otedola ya bayyana cewa shi da ake ƙoƙarin zargi yanzu, shi ne ya fara tona asirin almundahanar tallafin a gwamnatin Goodluck Jonathan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Hamshakin 'dan kasuwa, Femi Otedola ya musanta zargin da mai bai wa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Namadi Sambo, Umar Sani, shawara.

Umar Sani, ya bayyana cewa kamfanin Otedola na Zenon Petroleum da Gas ya taɓa cin gajiyar tsarin tallafin man fetur da aka soke a kasar nan.

Kara karanta wannan

Bayan wuya: Tinubu ya fadi yadda sauki ya fara samu wa Najeriya

Femi Otedola ya soki hadimin tsohon mataimakin Shugaban Kasa
Hoton hamshakin 'dan kasuwa, Femi Otedola Hoto: Femi Otedola
Source: Getty Images

Zarge-zargen sun fusata hamsahakin mai kudin, inda ya gaggauta mayar da martani ta cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin Otedola kan zargin badakalar mai

A cikin sakon, Femi Otedola ya bayyana cewa hankalinsa ya kai ga wani batu da Umar Sani ke yada wa, wanda ke danganta kamfaninsa da cin gajiyar tallafin mai fetur.

Ya bayyana cewa:

“Yana ƙoƙarin karkatar da gaskiya da kokarin bata min suna da hanyar dangantaka ni badakalar tallafin man fetur a kasar nan.
"Duk waɗannan kalaman ƙarya ne, marasa tushe, kuma ƙoƙari ne na yaudarar jama'a da sauya abin da ya faru."
Otedola ya fadi yadda su ka shirya wa 'dan majalisa gadar zare
Hoton fitaccen 'dan kasuwa a Najeriya, Femi Otedola Hoto: Femi Otedola
Source: Instagram

Hamshakin 'dan kasuwar ya nanata cewa kamfaninsa na 'Zenon Petroleaum and Gas' bai taba cin moriyar tallafin man fetur daga gwamnatin Najeriya ba.

A kalamansa:

“Zenon Petroleum and Gas Limited kamfani ne da ya taɓa shigo da dizal kaɗai, sama da 90% a kasuwa, kuma bai taɓa yin kasuwancin man fetur ba. Saboda haka ba zai taɓa yin ikirarin tallafi a ƙarƙashin tsarin talafin man fetur ba. An riga an cire Dizal daga tsarin tallafi."

Kara karanta wannan

Abin kunya: Malamin addini ya yaudari yar'uwa da ƙanwarta a wurin ibada, ya auka musu

Otedola ya bukaci wanke sunansa

Otedola ya ƙara bayyana cewa shi ne ya tona asirin cuwa-cuwar tallafin man fetur a lokacin gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, kuma akwai rahoto da ya tabbatar da haka.

Ya ce:

“Ni 'dan kwamitin tattalin arzikin Shugaba Goodluck Jonathan. Ni ne na fara sanar da Shugaban Kasa game da babbar badakalar da ake yi a tsarin tallafin man fetur. Da ya kira tsohuwar Ministar Man Fetur, ta musanta."
"Amma da na ga ba zan bari abin ya ci gaba ba, na kira Sanata Bukola Saraki na shaida masa. Shi kuma ya kai maganar gaban majalisar dattawa, daga nan majalisar wakilai ta fara bincike. Idan ni mai hannu ne a damfara, shin ni zan kai ƙarar kaina?”

A kan batun tsohon ɗan majalisa Farouk Lawan, Otedola ya ce:

“Da aka san ni ne mai tona asiri, sai masu hannu a damfarar suka fara mayar da martani ta hanyar amfani da kwamitin majalisa da Hon. Farouk Lawan ke jagoranta, suna ƙoƙarin tuhumata ba bisa ka’ida ba."

Kara karanta wannan

Za a shiga kotu da gwamna bayan kisan 'malami' da ya je yi masa wa'azi har gida

Ya ce sun shi da hukumar DSS ne su ka shirya wa dan majalisa Farouk Lawan gadar zare ta hanyar mika masa kudin cin hanci da aka riga aka yi wa alama.

Otedola ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya bayyana cikakken rahoton binciken Aig-Imoukhuede domin 'yan Najeriya su san ainihin abin da ya wakana.

Femi Otedola ya kare Aliko Dangote

A baya, mun wallafa cewa Hamshakin ɗan kasuwa Femi Otedola ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Aliko Dangote a rikicin da ya barke tsakanin matatarsa da kungiyar DAPPMAN.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Otedola ya ce kafa matatar Dangote za ta zama mafita ga matsalolin ƙasa game da samar da man fetur, amma DAPPMAN na son hana ruwa gudu.

Ya kuma yi sukar yadda DAPPMAN ke ƙoƙarin takure Dangote, inda ya ce lokaci ya yi da su daina dogaro da rumbunan ajiya mara amfani, su kusanci tsarin sayar da mai kai tsaye.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng