Za a Sheka Ruwan Sama da Iska Mai Karfi a Taraba, Zamfara da Wasu Jihohin Arewa
- NiMet ta yi hasashen ruwan sama da iska mai karfi zai sauka a a sassa daban-daban na Najeriya, musamman a Kudancin kasar
- Ebonyi, Cross River, Akwa Ibom, Enugu, Imo da Abia na cikin haɗarin ambaliya, inda aka bukaci jama'a su dauki matakan kariya
- NiMet ta gargadi direbobi su yi taka tsantsan yayin ruwan sama saboda matsalar ganin hanya da santsin titi da ka iya jawo haɗurra
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar kula da yanayi ta kasa (NiMet) ta fitar da sabon hasashen yanayi da zai yi aiki a ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025.
A cikin sabon hasahsen, NiMet ta ce akwai yiwuwar za a samu ruwan sama da iska mai karfi, hade da tsawa a sassa da dama na Najeriya.

Source: Original
Rahoton da NiMet ta wallafa a shafinta na X a daren ranar 30 ga Satumba, 2025 ya nuna cewa ruwan zai iya jawo cikas ga harkokin jama'a na yau da kullum.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hasashen ruwan sama a jihohin Arewa
A cewar rahoton, da safiyar Laraba, za a wayi gari da yanayi na rana tare da hadari, amma akwai yiwuwar a samu ruwan sama a wasu sassan Taraba da kudancin Adamawa.
Rahoton ya kara da cewa za a samu hadari da bullar rana a safiyar Laraba a sassan Abuja da jihohin Arewa ta tsakiyar Najeriya.
Sannan wasu sassan babban birnin tarayya, Neja, Kogi, Kwara da Nasarawa za su iya samun ruwan sama da iska mai karfi a safiyar ranar.
Da yamma kuma, ruwan sama da iska mai matsakaicin karfi za su shafi kudancin Zamfara, kudancin Kaduna, kudancin Bauchi, Kebbi, kudancin Gombe da kuma Taraba.
A Arewa ta Tsakiya ma, ana hasashen ruwan sama mai karfi zai sauka a mafi yawan jihohin shiyyar, abin da zai iya kawo tangarda ga zirga-zirgar jama’a da kuma ayyukan kasuwanci.
Hasashen ruwan sama a Kudancin Najeriya
A kudancin kasar kuwa, rahoton ya nuna cewa za a iya samun yanayi na hadari da ruwan sama lokaci zuwa lokaci a safiyar Laraba a jihohin Edo, Legas, Delta, Ogun, Ondo, Enugu, Imo, Ebonyi, Ribas, Cross River, Akwa Ibom da Bayelsa.
Da yammacin ranar kuma, ana sa ran ruwan sama da iska mai karfi a yawancin jihohin Kudancin Najeriya.

Source: UGC
Gargadi daga NiMet ga 'yan Najeriya
Hukumar NiMet ta yi gargadin yiwuwar ambaliyar ruwa a jihohin Ebonyi, Cross River, Akwa Ibom, Enugu, Imo da Abia.
Haka kuma, an shawarci direbobi da su yi tuki a hankali saboda ruwan sama mai karfi na rage hangen nesa, kuma titi na santsi, wanda zai iya jawo ambaliya.
An shawarci mazauna yankunan da aka yi hasashen za su samu ambaliya da su dauki matakan gaggawa don kare rayuka da dukiyoyinsu.
Kaduna: Ambaliya ta lalata gidaje, gonaki
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ambaliyar ruwa ta lalata gidaje da gonaki a garin Manchok, da ke masarautar Moro’a a karamar hukar Kaura ta jihar Kaduna.
Mazauna yankin wadanda suka rasa kayayyakin gida da amfanin gona, sun nemi agajin gaggawa daga wajen gwamnati.
Lamarin wanda ya jawo asarar dukiya da amfanin gona, ya sanya mazaunan yankin sun mika kokon bararsu yayin da suke jimamin asarar da suka tafka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


