An Yi Wa Tinubu Hannunka Mai Sanda kan Batun Takarar Jonathan a Zaben 2027

An Yi Wa Tinubu Hannunka Mai Sanda kan Batun Takarar Jonathan a Zaben 2027

  • Ana ci gaba da muhawara kan batun ko Goodluck Jonathan na da hurumin sake tsayawa takarar shugaban kasa
  • Fadar shugaban kasa ta fito ta bayyana cewa kotu ce za ta raba gardama kan hurumin Jonathan na sake yin takara
  • Sai dai, Denge Josef Onoh, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu kan ka da ya bari a yaudare shi ta hanyar gaya masa abin da ba haka yake ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Bayelsa - Tsohon kakakin shugaban kasa Bola Tinubu na yankin Kudu maso Gabas, Denge Josef Onoh, ya yi magana kan batun takarar Goodluck Jonathan a 2027.

Denge Josef Onoh ya tabbatar da cewa Goodluck Jonathan yana da hurumin tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaben 2027 bisa kundin tsarin mulki.

Jonathan na da hurumin sake tsayawa takara a 2027
Shugaban kasa Bola Tinubu tare da Goodluck Jonathan Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Goodluck Jonathan
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana da manema labarai a birnin Yenagoa, jihar Bayelsa, a ranar Talata, 30 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

Ta fara fashewa: Tinubu na shirin nada Farfesan Arewa a matsayin shugaban INEC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara aka ba Bola Tinubu?

Onoh ya bayyana cewa an riga an yanke hukunci kan hurumin Jonathan na sake yin takara a baya, kuma babu wanda ya kalubalanci hakan.

Maganganun Onoh sun biyo bayan jawabin hadimin Tinubu, Bayo Onanuga, a ranar Litinin, inda ya yi gargadin cewa kotu ce za ta yanke hukunci kan hurumin Jonathan na sake yin takara a zaben 2027.

Amma Onoh ya saba da Onanuga, inda ya tunatar da shi cewa an riga an kammala wannan batu, kuma an yanke hukunci wanda ya goyi bayan Jonathan.

Onoh ya ce al’ummar Najeriya ne kawai za su zaɓi wanda zai jagorance su, kuma gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ba za ta tauye hakkin kowanne ɗan adawa na tsayawa takara ba, rahoton The Guardian ya tabbatar da labarin.

“Saboda haka, bai kamata a ruɗi shugaban kasa Tinubu da labaran wasu mutane da ke gaya masa akasin hakan ba."

Kara karanta wannan

PDP ta raba gardama kan batun zaman Jonathan mamba a jam'iyyar

"Wannan shi ne abin da mutanen da ke kusa da Jonathan suka yi masa a lokacin shirin zaben 2015, suka sa ya yi imani cewa ba za a iya kayar da shi ba, cewa ‘yan Najeriya na kaunarsa, har ya yi sakaci bai hango Tinubu ba.”
"Tinubu ne wanda ya assasa rashin nasarar Jonathan a zaɓe. Bai kamata shugaban kasa ya faɗa cikin tarkon irin waɗannan mutanen da ke kewaye da shi yanzu ba."
"Muryar gaskiya guda ɗaya da ya kamata ya saurara ita ce ta uwargidansa, domin da yawa za su yaudare shi a watanni masu zuwa."

- Denge Josef Onoh

An ba Tinubu shawara kan Jonathan
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan tare da Mai girma Bola Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Me kotu ta ce kan hurumin Jonathan

Ya kara da cewa hukuncin kotu da aka yanke a watan Mayun 2022 na babban kotun tarayya a Yenagoa, jihar Bayelsa a sharia mai lamba FHC/YNG/CS/86/2022, ya tabbatar da cewa Jonathan yana da hurumin sake tsayawa takarar shugabancin Najeriya.

A cikin hukuncin, Mai shari’a Isa H. Dashen ya tabbatar da cewa Jonathan ya cancanci sake tsayawa takarar shugaban kasa a Najeriya bisa kundin tsarin mulki.

PDP ta tabo batun zaman Jonathan 'dan jam'iyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta yi karin haske kan matsayin Goodluck Jonathan a cikinta.

Kara karanta wannan

"Sai an je gaban kotu," Fadar shugaban kasa ta kara tabo batun takarar Jonathan a 2027

PDP ta bayyana cewa har yanzu tsohon shugaban kasan mamba ne a jam'iyyar domin bai fita ba.

Mai magana da yawun PDP, Debo Ologunagba ya bayyana cewa a saninau Jonathan yana cikin jam'iyyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng