Babbar Magana: Kotu ta bada Umarnin Kama Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu

Babbar Magana: Kotu ta bada Umarnin Kama Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu

  • Babbar Kotun Tarayya mai zama a Osogbo, babban birnin jihar Osun ta zargi shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu da raina umarninta
  • Alkalin kotun, Mai Shari'a Funmilola Demi-Ajayi ta umarcci Sufeto Janar na rundunar 'yan sanda ya kamo Yakubu idan ya ki aiwatar da hukuncinta
  • Kotun ta bai wa INEC da Yakubu kwanaki bakwai au wallafa sunayen shugabannin jam'iyyar AA a shafin yanar gizo na hukumar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osogbo, jihar Osun - Kotun Tarayya da ke zama a Osogbo, babban birnin jihar Osun, ta umurci a kama shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmoud Yakubu.

Kotun ta bai wa Sufeto Janar na ‘Yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, umarnin cafke Yakubu ne saboda raina umarnin kotu.

Shugaban hukumar zabe, Mahmud Yakubu.
Hoton shugaban hukumar zaben Najeriya, Farfesa Mahmud Yakubu Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

This Day ta rahoto cewa alkalin kotun, Mai shari’a Funmilola Demi-Ajayi, ce ta ba da umarnin yayin yanke hukunci kan rikicin jam'iyyar AA da hukumar INEC.

Kara karanta wannan

Ta fara fashewa: Tinubu na shirin nada Farfesan Arewa a matsayin shugaban INEC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meya sa kotu ta sa a cafke shugaban INEC?

Ta bayyana cewa Mahmoud Yakubu da INEC sun yi kuskure da rashin girmama hukuncin kotun na baya wanda ya umurce su su amince shugabannin jam'iyyar AA na jihohi.

Tun farko kotun ta umarci INEC ta amince da shugabannin AA da aka zaɓa ƙarƙashin jagorancin Adekunle Rufai Omoaje.

Lauyan Jam'iyyar AA, K.O Etibo, ya nemi a cike fom 48 da 49, tare da neman a daure Mahmoud Yakubu a kurkuku saboda kin bin hukuncin kotu.

Kotu ta bai wa INEC wa'adin mako guda

Kotun ta ba INEC da shugabanta wa’adin kwanaki bakwai su dawo da sunayen shugabannin jam'iyyar AA na jihohi da aka zaɓa ƙarƙashin jagorancin Omoaje a shafin yanar gizon hukumar.

Mai shari'a Funmilola Demi-Ajayi ta ce idan wa'adin mako guda ya kare INEC ba ta mayar da sunayen shugabannin AA ba, umarnin kama shugabanta zai fara aiki nan take.

A karshe, alkalin kotun ta amince da babban taron AA na kasa, wanda aka zabi Omoaje a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa tare da sauran mambobin NEC.

Kara karanta wannan

Sheikh Bala Lau ya hade 'yan Izala da Darika, ya masu nasiha mai ratsa zuciya kan Tinubu

Gudumar kotu.
Hoton gudumar kotu da ake tsawatarwa da ita Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Taron dai ya gudana ne a dakin karatu na tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, cewar rahoton Daily Post.

Kotun ta yanke hukuncin cewa taron ya inganta domin jami’an INEC sun halarta, kuma an gudanar da shi bisa tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar da dokokin zaɓe.

Tinubu na shirin nada sabon shugaban INEC

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara duba yiwuwar mika ragamar INEC ga Farfesa Joash Ojo Amupitan, SAN, dan asalin jihar Kogi a Arewacin Najeriya.

Wannan dai na zuwa me yayin da wa'adi na biyu kamar yadda doka ta tanada na shugaban INEC mai barin gado, Farfesa Mahmud Yakubu zai kare a watan Nuwamba, 2025.

Bincike ya gano cewa Farfesa Mahmud Yakubu ya shirya barin ofis tun watan Yuni, amma fadar shugaban kasa ta roƙe shi ya dakata a lalubo wanda zai gaje shi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262