Remi Tinubu Ta Tona irin Kalubalen da Tikitin Muslim Muslim Ya Jefa Ta kafin Kama Mulki
- Mai dakin Shugaban Kasa, Oluremi Tinubu ta bayyana halin da ta shiga a lokacin da mai gidanta, Bola Tinubu ke neman kujerar mulkin Najeriya
- A cikin wani littafi da ta rubutu, ta bayyana cewa zaɓin takarar shugaban ƙasa da Tinubu ya yi a kan tikitin “Muslim‑Muslim” ya raba kan cocinta
- Oluremi Tinubu ta ce bakin jinin da wannan lamari ya jawo bai hana ta ci gaba da bauta wa Ubangijinta ba, har aka samu nasara
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Uwar gidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa zaɓin da mijinta ya yi na takarar shugaban ƙasa a 2023 ya jawo mata matsala.
Ta ce zabin yin takara da Tinubu ya yi a kan tsarin tikitin Muslim Muslim ya jefa ta cikin mara dadi a cocinta, inda aka ware ta a gefe.

Source: Twitter
Punch ta ruwaito cewa Oluremi Tinubu ta bayyana haka a cikin sabon littafinta mai shafi 52 da ta fitar don murnar cikar shekaru 65 da haihuwa.
Tikitin Muslim-Muslim ya takurawa Oluremi Tinubu
Jaridar The Cable ta wallace cewa a cikin littafin da aka yi wa taken The Journey of Grace: Giving Thanks in All Things, Oluremi Tinubu ta ce cocinta ya dare.
Ta bayyana yadda cocin Redeemed Christian Church of God ya rabu gida‑gida, inda wasu suka yi watsi da ita saboda wannan zaɓi na maigidanta.
Sanata Oluremi ta bayyana cewa wannan ya nuna yadda jama'a ke da ra'ayin siyasa daban-daban duk da cewa coci guda su ke zuwa yin bauta.

Source: Twitter
Ta ce:
“Na gane haka a lokacin da ya ke nema a zabe ni Sanata, na kai hotunan yakin neman zabena, amma jama'a su ka yi biris da su. Daga wannan lokaci ban kuma irin wannan ba."
Yada Remi Tinubu ta zauna a cocinta
Mai dakin Shugaban Kasa ta bayyana cewa duk da wannan kiyayya da ta fuskanta saboda mai gidanta, wannan bai rage mata karsashi wajen bauta a cocin ba.
"Duk da wannan kiyayya, wasu na kara min kwarin gwiwa, musamman dattawan. Su kan ce na dage da addu'a."
Uwargidar ƙasa ta ce ba ta bar aikin cocin da ta yi tsawon shekaru 15 ba, inda ta tashi daga mai aiki zuwa Mataimakiyar Fasto a shekarar 2018.
Ta ce yawan zuwa coci da yin ibada na daga cikin abubuwan da su ka taimaka mata wajen samun nasara da kau da kai dga maganganun masu adawa da zabin Tinubu.
A cikin littafinta, ta bayyana yadda take yin yafiya ga duk waɗanda su ka ci amanar mijinta a lokacin yakin zaɓe na 2023.
Tinubu na shirin nada sabon shugaban INEC
A wani labarin, mun wallafa cewa rahotanni na nuni da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na nazarin nada Farfesa Joash Ojo Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar INEC.

Kara karanta wannan
"Za ku iya rasa kimarku": Tinubu ya aika da gagarumin saƙo ga Majalisar Ɗinkin Duniya
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wa'adin Farfesa Mahmud Yakubu ya kusa ƙarewa bayan ya kwashe kusan shekaru 10 yana jagorantar hukumar, kuma ana shirin maye gurbinsa.
Majiyoyi masu ƙarfi daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa sun samu tabbacin ana duba sunan Farfesa Amupitan, 'dan jihar Kogi a Arewacin Najeriua domin nadin nasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

