Ta Fara Fashewa: Tinubu na Shirin Nada Farfesan Arewa a Matsayin Shugaban INEC

Ta Fara Fashewa: Tinubu na Shirin Nada Farfesan Arewa a Matsayin Shugaban INEC

  • Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu na dab da nada wanda zai maye gurbin shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu
  • Wasu majiyoyi masu karfi sun bayyana cewa Tinubu ya fara karkata kan Farfesa Joash Ojo Amupitan, SAN, dan asalin jihar Kogi
  • Wannan na zuwa ne yayin da wa'adin Mahmud Yakubu ke dab da karewa bayan kammala zango biyu tun bayan nadinsa a 2015

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ga dukkan alamu batun nemo wanda zai maye gurbin Farfesa Mahmud Yakubu a matsayin shugaban hukumar INEC ta kasa ya zo karshe.

Rahotanni sun nuna cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara duba yiwuwar mika ragamar INEC ga Farfesa Joash Ojo Amupitan, SAN, dan asalin jihar Kogi a Arewacin Najeriya.

Shugaban kasa, Bola Tinubu.
Hoton Mai Girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya Hoto: @OfficialABAT
Source: Facebook

Wasu majiyoyi masu karfi sun tabbatar da hakan ga jaridar This Day jiya da daddare bayan an tuntube su kan batun nadin shugaban hukumar INEC.

Kara karanta wannan

Tajudeen: Shugaban majalisa ya hango lokacin kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu na shirin nada shugaban INEC

Da aka tambayi wani babban jami’i a fadar shugaban kasa kan ko gaskiya ne Tinubu na duba yiwuwar maye gurbin shugaban INEC mai barin gado, Yakubu da Farfesa Amupitan, ya amsa da cewa, "Eh, tabbas."

Haka kuma wani aminin Amupitan ya tabbatar da labarin, inda ya ce ko da yake ba shi da tabbacin an sanar da nadin a hukumance, amma yana dai ana nazari kansa.

Bukatar maye gurbin Mahmud Yakubu ta taso ne sakamakon karewar wa’adin mulkinsa a hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC.

Wa'adin Mahmud Yakubu ya zo karshe a INEC

An nada shi tun a 2015 lokacin Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, kuma yanzu kusan ya kammala wa’adi biyu, watau shekaru 10.

Bincike ya gano cewa Farfesa Mahmud Yakubu ya shirya barin ofis tun watan Yuni, amma fadar shugaban kasa ta roƙe shi ya dakata a lalubo wanda zai gaje shi.

Kara karanta wannan

Sheikh Bala Lau ya hade 'yan Izala da Darika, ya masu nasiha mai ratsa zuciya kan Tinubu

Mahmud Yakubu ya kawo sauye-sauye domin inganta tsarin zabe, kodayake ya sha suka musamman kan matsalolin hukumar INEC ta rika samu da ayyana zabe a matsayin wanda bai kammalu ba watau “inconclusive.”

Ci gaban INEC a karkashin Mahmud Yakubu

Daga cikin sababbin abubuwan da ya kawo akwai tantancewa da kada kuri’a lokaci guda da na'urar tantancewa ta BVAS) wadda ta maye gurbin na'urar Card Reader.

Bugu da kari, Mahmud Yakubu ne ya kirkiro shafin INEC na tattara sakamakon zabe ta yanar gizo IRev wanda ke bai wa jama’a damar kallon sakamakon daga rumfunan zabe kai tsaye.

Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmud Yakubu.
Hoton shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmud Yakubu Hoto: @INECNigeria
Source: Twitter

Idan aka tabbatar da nadinsa, Farfesa Amupitan zai ja ragamar gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra da aka shirya yi a ranar 6 ga Nuwamba, 2025.

Zai kuma jagoranci zaben kananan hukumomin Abuja a ranar 21 ga Fabrairu, 2026; zaben gwamnan jihar Ekiti da na jihar Osun da za a yi a 2026; da kuma babban zaben 2027.

Matakan da ake bi a nada shugaban INEC

A wani labarin, mun kawo maku matakan da ake bi bisa tanadin doka wajen nada shugaban hukumar INEC na kasa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi dalilin da ya sa 'yan Najeriya ke shan wuya a gwamnatinsa

Wa'adin shugaban INEC mai ci, Farfesa Mahmud Yakubu zai kare ne a watan Nuwamba, 2025, wanda bisa doka Shugaban Kasa zai nada wanda zai maye gurbinsa.

Legit Hausa ta kawo muku cikakken rahoto kan hanyoyi ko matakan da ake bi wajen nada shugaban hukumar zabe a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262