Rajistar Zaben 2027: Borno Ta Sha Gaban Osun da Legas, Kano na Baya har yanzu
- Hukumar INEC ta bayyana cewa fiye da mutane miliyan 6.2 sun kammala rajistar farko ta yanar gizo cikin mako shida
- Borno ta samu matsayi na farko da mutum 682,805 yayin da Osun da Lagos suka koma matsayi na biyu da na uku
- Matasa ‘yan shekaru 18 zuwa 34 ne suka fi yawa, inda suka kai sama da miliyan 4 a cikin jerin sababbin masu rajista
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar da sabon rahoto bayan shafe mako shida da fara rajista domin mallakar katin zabe.
Rahoton ya nuna cewa Borno ta zarce Osun da Lagos wajen yawan mutane da suka kammala rajistar farko ta yanar gizo a cikin shirin rajistar masu kada kuri’a na CVR.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai kan yadda rajistar ke gudana ne a wani sako da hukumar INEC ta wallafa a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya nuna cewa a tsakanin 22 zuwa 28 ga Satumba, 2025, an samu jimillar mutane 6,232,673 da suka yi rajista.
Daga cikin wannan adadi, mata suka fi yawa da 52.15%, inda suka kai 3,250,338, yayin da maza suka kai 2,982,335, daidai da 47.85%.
Jihar Borno ce ta 1 a rajistar katin zabe
Borno ta zama kan gaba da mutum 682,805 da suka yi rajistar farko, lamarin da ya bata matsayi na farko a jerin jihohi.
Punch ta wallafa cewa jihar Osun ta zo ta biyu da mutum 599,363, sai Lagos da mutum 555,442 da suka yi rajista.
Kano ta biyo bayan Ogun da Kogi
Jihar Kebbi ta samu matsayi na hudu da mutum 472,662, sai Ogun da 450,897 da Kaduna da 376,054.
A daya bangaren, Kogi ta biyo da 298,194, sannan Kano da mutum 290,690, Yobe ta samu 258,693, yayin da Babban Birnin Tarayya (Abuja) ya yi rajistar mutum 227,397.
Oyo, Jigawa, Zamfara, Katsina da Sokoto duk sun shiga cikin jerin jihohi da suka yi rajista sosai, sai dai jihohin Kudu maso Gabas kamar Ebonyi, Abia da Enugu sun samu adadi kadan.
Rahoton hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ya nuna cewa jihar Enugu ta yi rajistar mutum 5,092 ne kacal.

Source: Getty Images
Adadin matasa da dalibai a CVR
Matasa 'yan shekaru 18 zuwa 34 sun mamaye jerin da mutane 4,230,715, wanda ya nuna muhimmancin rawar da suke takawa a zabubbukan Najeriya.
Dalibai sun kai sama da miliyan 1.5 a cikin jerin, yayin da mutane masu bukata ta musamman suka kai 137,865.
Tun bayan fara rajistar a ranar 18, Agusta, 2025, jihohin Kudu maso Yamma kamar Osun, Lagos da Ogun suka dade suna kan gaba.
Amma yanzu rahoton ya nuna cewa Arewacin Najeriya, musamman Borno da Kebbi, sun karu sosai sakamakon wayar da kan jama’a daga kungiyoyin al’umma.

Kara karanta wannan
'Yar Najeriya da ta shirya kafa tarihin kwanciya da maza 100 a awa 24 ta canza shawara
Maganar ADC, PDP kan shugaban INEC
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyun siyasa sun yi magana kan wanda suke so ya zamo sabon shugaban INEC.
Hakan na zuwa ne yayin da wa'adin shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu zai kare a watan Nuwamban 2025.
Jam'iyyun ADC da PDP sun bukaci shugaban kasa da ya zabi mutum mai nagarta da zai kare muradun kasa yayin zabuka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

