Gwamna Abba Kabir Ya Aika da Muhimmin Sako ga Jami'an Gwamnatinsa
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci jami'an gwamnatinsa da masu rike da mukaman siyasa su yi abin da ya dace
- Abba Kabir Yusuf ya nuna muhimmancin da ke tattare da sauke nauyin da aka dora musu yadda ya kamata
- Gwamnan ya nuna cewa bai kamata a ci amanar mutanen da suka ba shi kuri'unsu a zaben shekarar 2023
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi kira da babbar murya ga jami'an gwamnatinsa.
Gwamna Abba ya bukaci masu rike da mukaman siyasa da manyan ma’aikatan gwamnati da su sanya gaskiya da rikon amana a matsayin ginshikin aikinsu.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
Da sauran rina a kaba: Gwamna Abba ya yi maganar cikar Najeriya shekara 65 da 'yanci
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kano ta shirya taro a Kaduna
Gwamna Abba ya bayyana hakan ne wajen wani taron horaswa na kwana uku wanda aka shirya tare da haɗin gwiwar ANHI Consultants International da gwamnatin jihar Kano a Kaduna.
Ya jaddada cewa gaskiya da amana su ne ginshikan kyakkyawar gwamnati.
Wace shawara Gwamna Abba ya bada?
Abba Kabir Yusuf ya umurci mahalarta taron da su tabbatar cewa kowane aiki, shawara, da manufofi suna cike da gaskiya da amana.
Ya ce samar da nagarta zai tabbatar da makoma mai kyau ga al’ummomi masu zuwa.
Yayin da yake gargadi kan cin hanci, gwamnan ya jaddada cewa rashawa na cutar da talakawa da marasa galihu, yana mai cewa mutanen Kano sun fara gajiya da alkawurran da ba a cikawa.
"Suna son aiki da ganin sakamako. Suna son gwamnati da za ta yi aiki a gare su, ba wadda za ta wadatar da kaɗan ba. Shi ya sa suka zaɓe mu a 2023, kuma bai kamata mu ci amanarsu ba."
- Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kara da cewa nasarar gwamnati tana dogara ne ga kyakkyawan tsari da kuma gaskiya da kwarewar waɗanda aka ba amanar aiwatar da manufofinta.
Ya karfafa jami’an gwamnatinsa da su kasance masu karfin hali da jajircewa wajen yin abin da ya dace duk da kalubalen da za su fuskanta.
Masana sun yi jawabi a wajen taron
Taron horaswar ya kunshi jawabai daga masana, ciki har da Dr. Aminu I. Gusau, wanda ya bayyana tawagar gwamnan a matsayin masu kwarewar jagorantar Kano

Source: Facebook
Shugaban ma’aikata fadar gwamnati, Dr. Sulaiman Sani, da sakataren gwamnati, Alhaji Umar Farooq, su ma sun yaba da jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Sun bayyana cewa gwamnatinsa ta cin ma nasararori cikin shekara biyu wadanda wadda ta gabace ta ba ta cinmawa ba a shekara takwas.
Gwamna Abba ya mika sunayen kwamishinoni
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mika sabuwar bukata ga majalisar dokokin jihar.

Kara karanta wannan
Bayan yin garambawul, Gwamna Abba ya mika sunaye ga majalisa don nada kwamishinoni
Gwamna Abba ya mika sunayen mutane biyu da yake son majalisar ta amince da su don zama kwamishinoni a gwamnatinsa.
Mutane biyun da aka mika sunayensu gaban majalisar sun fito ne daga kananan hukumomin Minjibir da Bichi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
