Rikicin Dangote da PENGASSAN: Ndume Ya Bukaci Tinubu Ya Ɗauki Mataki mai Tsauri

Rikicin Dangote da PENGASSAN: Ndume Ya Bukaci Tinubu Ya Ɗauki Mataki mai Tsauri

  • Ali Muhammad Ndume ya shawarci Shugaban Kasa a kan rikicin kungiyar PENGASSAN da Matatar Dangote 
  • Sanata Ndume ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya rushe kungiyar PENGASSAN baki dayan ta kowa ya huta 
  • 'Dan majalisar ya zargi kungiyar da ketare iyakarta wajen neman tilasta wa kamfanin Dangote bin umarninta

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Sanata Ali Ndume, wanda ke wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauki mataki a kan PENGASSAN.

Ya ce alamu suna nuna cewa kungiyar manyan ma'aikatan mai ta PENGASSAN na bibiyar Matatar Dangote saboda biyan bukatar kashin kai.

Ndume ya shawarci Tinubu a kan PENGASSAN
Hoton Shugaba Bola Tinubu tare da Dangote Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Ndume ya shawarci Tinubu da ya rushe kungiyar manyan ma’aikatan man fetur ta Najeriya (PENGASSAN)

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga rikicin Dangote da PENGASSAN, ya fadi abin kunyar da zai faru ga Najeriya

Shawarar Ndume ga Tinubu kan PENGASSAN 

Daily Trust ta wallafa cewa Ndume ya ba Tinubu shawarar rushe PENGASSAN idan kungiyar ta ci gaba da ɗaukar matakan da ke kare muradun kashin kanta a kan Matatar Dangote.

Ndume ya bayyana cewa matakin kungiyar na shiga yajin aikin ƙasa baki ɗaya bayan sallamar ma’aikata 800 a kamfanin Matatar Dangote, ya nuna tana son tilasta iko kan harkar da ba ta da hurumi.

Ya ce:

“Kamata ya yi PENGASSAN ta kare muradun ‘yan Najeriya. Amma abin da suka yi na kama hanyar kare kansu ne kawai. Dangote kamfani ne mai zaman kansa. Ba za ka zo ka ce kana tilasta masa wani abu ba."
Ndume na son Tinubu ya dauki mataki a kan PENGASSAN
Hoton Shugaba Bola Tinubu da Sanata Ali Ndume Hoto: Bayo Onanuga/Senator Ali Muhammad Ndume
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa: 

“Wannan ƙasa mai ‘yanci ce. Ba za ka tilasta wani ya shiga kungiyarka ba. Ma’aikatan ba su mallaki man fetur da iskar gas na Najeriya ba, don haka ba za su riƙa neman abu fiye da wadanda suka mallaka ba.” 

Kara karanta wannan

PENGASSAN: Ana zaman dar dar kan karancin fetur da rashin wuta a Najeriya

Ndume ya caccaki PENGASSAN a kan Dangote 

Ya bukaci Shugaba Tinubu ya ɗauki mataki mai tsauri ganin yadda a cewarsa, kungiyar tana kawo cikas ga ci gaban yan Najeriya.

Ndume ya ce:

"Ina suka shiga lokacin da gwamnati ta cire tallafin mai? Ina suka shiga lokacin da farashin mai ya kai N1000? Ina suka shiga lokacin da matatun ƙasa suka daina aiki?” 

Ya shawarci shugaban ƙasa da ya yi amfani da ikon sa na gudanarwa wajen kawo karshen rikicin, inda ya ce: 

“Mafi alheri shi ne shugaban ƙasa ya sanya hannu a kan wata doka ya dakatar da su. Yana da ikon rushe su. A wannan yanayin, bana damuwa ko ya yi kama da mai mulkin kama-karya, saboda wasu lokuta na bukatar matakai masu tsauri.”  

A halin yanzu dai, gwamnatin tarayya ta shiga tsakani domin sasantawa tsakanin kamfanin Dangote da kungiyar PENGASSAN don kawo karshen rikicin.  

Ana zaman dar-dar kan yajin aikin PENGASSAN

A wani labarin, mun wallafa cewa Najeriya na dab da fadawa cikin wani babban rikici na tattalin arziki da jin dadin al'umma, sakamakon yajin aikin da PENGASSAN ta fara.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta kira PENGASSAN da Dangote, za a hau teburin sulhu

PENGASSAN ta bayar da umarni ga dukkannin ‘ya’yanta a fadin kasar nan da su dakatar da aiki tun daga ƙarfe 12:01 na safiyar Litinin, sakamakon sabani da Matatar Dangote.

PENGASSAN ta zargi matatar man Dangote da karya dokokin kwadago na gida da na kasa da kasa bayan ta sallami ma'aikata akalla 800 daga bakin aiki a karshen mako.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng