Gwamna Sule Ya Gayawa Gwamnonin Arewa Gaskiya kan Rashin Tsaro
- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana cewa gwamnatocin jihohi na samun kudade masu kauri daga asusun tarayya
- Abdullahi Sule ya nuna cewa kudin da ake samu a yanzu sun ninka wadanda ake gwamnatocin Najeriya suke rabawa a shekarun baya
- Bisa hakan ne sai ya shawarci gwamnonin Arewa su maida hankali wajen magance matsalar rashin tsaro da ya fitini al'umma
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce yanzu gwamnatocin jihohi a Najeriya suna da wadatattun kuɗaɗe fiye da yadda suke da su a baya.
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana cewa wajibi ne a karkatar da kudin zuwa sassan da za su iya sauya tattalin arzikin kasar nan.

Source: Facebook
Jaridar TheCable ta ce Gwamna Sule ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin taron Northern Nigeria Investment and Industrialisation Summit (NNIIS) 2025 da aka gudanar a Abuja.
Gwamna Sule ya ce gwamnoni na samun tulin kudi
Ya ce kudin da ake rabawa tsakanin matakai uku na gwamnati sun ninka sau huɗu sakamakon gyare-gyaren da Shugaba Bola Tinubu ya aiwatar, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar da labarin.
"A karon farko cikin tarihinmu, dukkan matakan gwamnati suna samun kuɗi fiye da yadda suka taɓa tsammani."
"Sama da Naira tiriliyan 2.2 aka raba a wannan watan kaɗai. Lokacin da na zama gwamna a 2019, muna raba tsakanin biliyan 590 zuwa biliyan 620. Yau kuwa, adadin ya ninka sau huɗu."
- Gwamna Abdullahi Sule
Me gwamnatin Nasarawa ke yi?
Yayin da ya ke kara bayani a wajen taron, gwamnan ya ce Nasarawa ta yi amfani da gyare-gyaren da aka yi wajen tilastawa masu saka jari a sashen ma’adanai su kafa masana’antar sarrafa ma’adanai.
Gwamna Sule ya ce lamarin ya kai ga kaddamar da masana’antar da ke sarrafa tan 3,000 a kowace rana, tare da kammala wata babbar masana’antar da za ta sarrafa tan 6,000 a rana wacce ake jiran a kaddamarwa.
Haka kuma ya tabbatar da kasancewar filayen mai a jihar da ake hasashen suna ɗauke da akalla gangar mai miliyan biyar zuwa bakwai.
Sannan ya bayyana shirin faɗaɗa gonakin shinkafa daga hekta 3,300 zuwa akalla hekta 8,000 kafin ƙarshen wa’adin mulkinsa.

Source: Facebook
Wace shawara ya ba gwamnonin Arewa?
Gwamna Sule ya shawarci gwamnonin Arewa da su maida hankali kan abin da kowace jiha ta fi kwarewa a kai, su ɗauki alhakin tsaron jihohinsu, kuma su guji dora laifi a kan wasu.
"Yanzu kowace jiha na da kudin da za ta iya kare mutanenta. Ya kamata mu daina zargin wani game da tsaro. Idan akwai wanda za a zarga, to kanmu za mu zarga."
- Gwamna Abdullahi Sule
Ya kamata gwamnoni su tashi tsaye
Kabir Bello ya shaidawa Legit Hausa cewa lallai ya kamata gwamnoni su tashi tsaye domin yin hubbasa wajen magance matsalolin da ke addabar jihohinsu.
"Mu a Katsina a fannin tsaro an samar da rundunar C-Watch, kuma tabbas suna taimakawa sosai."
"Gwamnati ta ba su makamai da kayan aiki kuma suna kokari wajen samar da tsaro. Sai dai akwai bangarorin da ya kamata a kara inganta su."

Kara karanta wannan
Bayan Tinubu ya maido shi ofis, Fubara ya dauki mataki mai tsauri a kan kwamishinoninsa
- Kabir Bello
'Yan bindiga sun sace hadimin gwamnan Nasarawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun yi awon gaba da daya daga cikin hadiman gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule.
'Yan bindigan sun sace mataimaki na musamman ga Gwamna Sule kan harkokin jin kai, Dr. Muhammed Egye Osolafia, wanda aka fi sani da Deedat.
Tsagerun sun yi awon gaba da shi ne a wani farmaki da suka kai a gidansa da ke cikin birnin Lafia.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

