Gwamna Ya Gwangwaje Magidanta da Tallafi bayan Tsuntsaye da Kwari Sun Tafka Barna

Gwamna Ya Gwangwaje Magidanta da Tallafi bayan Tsuntsaye da Kwari Sun Tafka Barna

  • Gwamna Babagana Umaru Zulum ya tallafawa mutanen yankin Dikwa sakamakon jarabawar da suka fuskanta a gonakinsu
  • Zulum ya zakulo magidanta 18,000, ya raba masu buhunan shinkafa da dawa domin rage masu radadin halin da suke ciki
  • Haka zalika gwamnan ya rabawa mata tallafin N10,000 a Dikwa, duk a wani bangare na kokarin tallafawa marasa karfi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya raba kayan abinci kyaita ga magidanta 18,000 a garin Dikwa, da ke tsakiyar jihar.

Raba wannan tallafin ya gudana a harabar fadar Shehun Dikwa sakamakon ibtila'in da ya afkawa amfanin gonakin mazauna yankin.

Gwamnan Borno, Babagana Umaru Zulum.
Hoton Gwamna Zulum a wurin rabon tallafin kayan abinci a Borno Hoto: @dauda_iliya
Source: Twitter

Tsuntsaye da kwari sun lalata gonaki

Leadership ta tattaro cewa manoma sun fuskanci annobar tsuntsaye da kwari irin su quelea birds da suka lalata mafi yawan gonakin da jama’ar yankin ke dogaro da su wajen rayuwa.

Kara karanta wannan

Bayan yin garambawul, Gwamna Abba ya mika sunaye ga majalisa don nada kwamishinoni

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Zulum, wanda ya jagoranci rabon kayan a ranar Litinin, ya bayyana damuwarsa matuƙa ga wadanda lamarin ya shafa.

Ya ce wannan matakin ya zama dole domin guje wa ƙalubalen yunwa da wadanda suka rasa amfanin gona ka iya shiga nan gaba.

Matakan da gwamnatin Borno ta dauka

Gwamna Zulum ya jaddada cewa gwamnatinsa ta ɗauki matakai na ƙarfafa harkar noma, musamman wajen yaƙi da ƙwari, don rage yawan asarar da manoma ke fuskanta.

“Rabon da mu raba kayan abinci a Dikwa kusan shekara ɗaya da rabi kenan. Saboda mun yi imani da cewa an samu ci gaba a tsaro, kuma jama’a sun fara komawa gonakinsu, hakan yasa muka rage yawan tallafin jin kai da kashi 90.
“Amma da safiyar yau mun zo Dikwa domin tallafa wa jama'a saboda fari da ya shafe su a bara. Kwari da tsuntsaye sun lalata gonakinsu, wanda hakan ya janyo manoma sun yi asarar amfanin gona mai yawa.”

Kara karanta wannan

"Za a yi 'yar kure," An fara zama kan zargin Sheikh Triumph da taba mutuncin Annabi SAW

- In ji Gwamna Babagana Zulum.

Yayin jawabi ga waɗanda suka amfana, Gwamna Zulum ya nuna farin ciki da yadda mazauna garin suka rungumi harkar noma a wannan daminar.

Yadda Zulum ya raba kudi da kayan abinci

Bugu da ƙari, gwamnan ya raba sama da Naira miliyan 350 ga mata 35,000 a Dikwa a matsayin tallafin gaggawa ga marasa karfi, rahoton jaridar Gazette.

Kowacce mace daga cikin 35,000 ta samu N10,000 da atamfa, baya ga buhunan shinkafa biyu da dawa guda biyu da kowane magidanci daga cikin 18,000 ya karɓa.

Gwamna Babagana Umaru Zulum.
Hoton buhunan dawa da shinkafa da Gwamna Zulum ya rabawa magidanta a Borno Hoto: @ProfZulum
Source: Twitter

Zulum ya samu rakiyar shugaban kwamitin rabon tallafin jin kai na jihar Borno, Injiniya Bukar Talba da dan majalisar dokoki mai wakiltar Dikwa, Zakariya Mohammed.

Sauran wadanda suka raja gwamnan su ne, Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, Sugun Mai Mele, tare da wasu manyan jami’an gwamnati.

Gwamna Zulum ya tallafa wa dalibai 90

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwarsa kan karancin yawan ɗaliban da ke shiga makarantar boko.

Kara karanta wannan

Kazamin rikicin manoma ya firgita Darazo, ya hana zuwa gona a Bauchi

Domin magance wannan matsala, Gwamna Zulum ya amince da biyan kuɗin tallafi na N300,000 ga iyayen ɗaliban guda 90.

Gwamnan ya dauki wannan mataki ne da nufin kara yawan masu shiga makaranta a Arewacin jihar Borno.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262