An Tono Badakalar Biliyoyi da ake Zargin Ganduje da 'Ya'yansa Sun Yi a Kano
- Rahoto na zargin cewa tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya fitar da 20% na jihar daga mallakar tashar tsandaurin Dala
- Wani bincike ya yi zargin cewa ‘ya’yan Ganduje da abokinsa sun shiga matsayin shugabanni da masu hannun jari a kamfanin
- Gwamnatin Kano ta yanzu ta ce har yanzu tana ita ce da mallakin kaso 20 na kamfanin tare da alkawarin bincikar lamarin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Wani bincike ya zargi tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da badakalar mallakar sashen tashar tsandaurin Dala.
An bayyana cewa Ganduje ya cire hannun jarin jihar Kano na kashi 20 cikin 100 daga kamfanin ya mayar da shi ga hannayen wasu.

Source: Twitter
Rahoton Premium Times ya ce kafin saka sunan wasu a kamfanin, Ganduje ya sanya ‘ya’yansa uku a matsayin daraktoci da masu hannun jari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya haifar da tambayoyi masu yawa kan halaccin yadda aka fitar da jihar daga mallakar kamfanin, musamman ganin cewa tun 2006 gwamnatin Kano ce ta mallaki 20%.
Yadda Kano ta samu 20% a tashar Dala
Tashar tsandaurin Dala ta samo asali ne tun 2003 karkashin jagorancin ɗan kasuwa Ahmad Rabiu.
Rahotanni sun bayyana cewa a 2006 gwamnatin Kano ta saye 20% karkashin mulkin malam Ibrahim Shekarau.
Sai dai gwamnatocin Shekarau da Rabiu Kwankwaso ba su aiwatar da alkawarin samar da abubuwan more rayuwa da aka ayyana musu ba.
Sahara Reporters ta rahoto cewa bincike ya nuna cewa wannan ya sa babban abokin hulɗa na kasar waje, Maersk Sealand, ya janye daga shirin.
Shigar Ganduje da sauya mallaka
A shekarar 2019, hukuma mai lura da shige da fice ta Najeriya ta yi barazanar janye yarjejeniyar gina tashar saboda tsaikon cigaba.
Wannan barazana ta sa Ahmad Rabiu ya mika 60% zuwa hannun iyalan tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje.
Daga baya a 2020, an tabbatar da cewa ‘ya’yan Ganduje, Abdulaziz, Umar da Muhammad sun zama daraktoci tare da abokinsa Abubakar Bawuro, inda kowannensu ke da 20% a kamfanin.

Source: Twitter
Wannan sabon tsarin ya kawar da gwamnatin Kano gaba ɗaya daga mallakar wani sashe na kamfanin.
A cikin wannan lokaci ne Ganduje ya amince da biyan fiye da Naira biliyan 2.3 don samar da abubuwan more rayuwa a tashar, kwangilar da daga baya ta kai sama da Naira biliyan 4.
Martanin gwamnatin Kano kan tashar
A cewar lauya Ibrahim Idris, ya kamata cire hannun jarin jiha daga kamfani ya bi matakai na doka, ciki har da amincewar majalisar zartarwa ko majalisar dokoki.
A yanzu, gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta Kano ta yi watsi da sabon tsarin mallakar kamfanin, tana mai cewa har yanzu jihar na da 20% na hannun jarin da aka saya tun 2006.
Daraktan zuba jari na ma’aikatar kasuwanci, Bashir Uba, ya tabbatar da cewa babu wani shaidar doka da ke nuna jihar ta sayar da mallakar hannayenta.
Ganduje ya yi wa Abba Kabir raddi
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi martani kan biyan bashin 'yan fansho da Abba Kabir Yusuf ya yi.
Mutane da dama, musamman 'yan Kwankwasiyya da NNPP na ganin cewa Ganduje ya gaza biyan 'yan fansho a lokacinsa.
Sai dai a wani martani da ya yi, tsohon gwamnan ya ce aikin gwamnati ya gaji haka dama, kuma Abba ma zai iya barin bashi ga wanda zai biyo bayansa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


