PENGASSAN: Ana Zaman Dar dar kan Karancin Fetur da Rashin Wuta a Najeriya
- 'Yan kasuwa da sauran mazauna kasar sun fara zaman fargaba a kan yajin aikin PENGASSAN ta tsunduma sabda rikicinta da Dangote
- A wani bangaren kuma kamfanonin wutar lantarki sun fara rufewa, sakamakon yadda yajin aikin ya fara taba yadda su ke ayyukansu
- 'Yan kasuwa sun yi gargadi kan tabarbarewar lamarin fetur da fargabar cewa farashin mai iya tashin gwauron zabo idan ba a dauki mataki ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Najeriya na dab da shirin fada wa a cikin mummunan rikici sakamakon halin da kasar nan ke kokarin shiga sakamakon yajin aikin PENGASSAN.
Kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta kasa (PENGASSAN) ta fara yajin aiki a ranar Litinin, 29 ga Satumba, 2025 bayan samun sabani da matatar Dangote.

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta ruwaito cewa kungiyar ta bayar da umarni ga dukkannin 'ya'yanta a fadin kasa da su dakatar da aiki tun daga ƙarfe 12:01 na safiyar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilan da ya jawo yajin aikin PENGASSAN
Legit ta ruwaito cewa PENGASSAN ta zargi matatar man Dangote da keta dokokin kwadago na Najeriya da na kasa da kasa, inda ta sallami ma’aikata fiye da 800 saboda shiga kungiyar kwadago.
Kungiyar ta bayyana cewa matakin ya saba wa yarjejeniyar aikin, kuma ana maye gurbin ‘yan Najeriya da ‘yan kasashen waje.
A cikin wata sanarwa da Sakatare Janar na kungiyar PENGASSAN, Lumumba Okugbawa, ya fitar, ya ce:
“Dukkanin ayyukan samar da iskar gas zuwa matatar Dangote su tsaya nan take. Dukkannin rassan kamfanonin mai na kasa su dakatar da samar da iskar gas zuwa matatar Dangote.”
Kungiyar dillalan mai ta kasa (IPMAN) ta yi gargadi cewa wannan yajin aiki zai iya haifar da hauhawar farashin man fetur da kuma kara tabarbarewar wutar lantarki a kasar.
An yi gargadi kan yajin aikin PENGASSAN
Haka zalika, Joy Ogaji, Sakatariyar Kungiyar Kamfanonin Samar da Wutar Lantarki (GenCos), ta tabbatar da cewa kamfanonin gas sun bayar da umarnin a rufe dukkanin tashoshin wutar lantarki da ke amfani da iskar gas.

Source: Getty Images
Ta ce:
“Wutar lantarki da ake samarwa da ruwa kadai ba zai iya daukar nauyin samar da wuta a Najeriya ba."
A halin yanzu, kungiyoyin da masu ruwa da tsaki sun bukaci gwamnatin tarayya da hukumar DSS da su shiga tsakani don warware rikicin kafin ya rikide zuwa matsalar kasa.
Gwamnati ta kira PENGASSAN da Dangote
A baya, mun wallafa cewa Gwamnatin tarayya ta nuna damuwa sosai game da rikicin da ya barke tsakanin kungiyar ma’aikatan mai ta kasa, PENGASSAN da matatar Dangote.
Saboda haka, Ministan Kwadago da Ayyuka, Maigari Dingyadi, ya kira shugabannin bangarorin biyu don halartar taron sulhu da za a gudanar domin sasanta al’amura.
Dingyadi ya bayyana cewa yajin aikin da PENGASSAN ta tsara zai iya yin sanadiyyar matsaloli ga tattalin arziki da kuma harkokin tsaro, saboda haka ta nemi a hau teburin sulhu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

