'Mu ne Farko': 'Yan Addinin Gargajiya Sun Kalubalanci Malaman Musulunci bayan Shirin Korarsu

'Mu ne Farko': 'Yan Addinin Gargajiya Sun Kalubalanci Malaman Musulunci bayan Shirin Korarsu

  • Fitacciyar mashahuriyar mai bin addinin gargajiya, Yeye Osunfunmilayo Ajile, ta ce ba za ta bar asalin addinin gargajiya ba
  • Ajile ta ce malamai daga wasu unguwanni sun mamaye gidanta suna neman ta bar Ilorin, amma ta nace da cewa tana da 'yancin addini
  • Ta bayyana cewa ibadarta ta kawo tsaro ga al'umma, tana kara da cewa ta kai rahoto ga ‘yan sanda

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ilorin, Kwara - Mabiya addinin gargajiya a jihar Kwara sun yi korafi kan malaman Musulunci da suka yi musu barazana.

Aare Olomitutu Odo Gbogbo l’Agbo na Kwara, Yeye Osunfunmilayo Ajile, ta ce ba za ta bar asalin addinin gargajiyarta ba ko meye za a ce.

An kaure da fada tsakanin malaman Musulunci da mabiya addinin gargajiya
Taswirar jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Malamai sun bukaci korar mabiya addinin gargajiya

Rahoton Punch ya tabbatar da cewa Ajile ta ce addinin gargajiya shi ne na farko a Ilorin tun kafin zuwan sauran addinai.

Kara karanta wannan

Kazamin rikicin manoma ya firgita Darazo, ya hana zuwa gona a Bauchi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta bayyana haka bayan arangama da wasu malamai Musulmi da suka mamaye gidanta, suna cewa ta bar yankin saboda ibadarta ta gargajiya.

Rahotanni sun nuna rikici ya barke a Ilorin ranar Litinin, 22 ga Satumbar 2025, lokacin da malamai daga Oke Odo, Danialu, da Gaa Akanbi suka kai mata hari

Bidiyon lamarin da ke yawo a yanar gizo ya nuna malaman Musulunci suna matsa mata ta bar unguwar, amma ta nace tana kare 'yancin addininta.

Ajile ta ce an gaya mata ta koma jihar Osun, amma ta ce:

"Ni 'yar Ilorin ce, an haife ni a nan, babu wanda zai kore ni."
Mabiya addinin gargajiya sun kalubalnaci malaman Musulunci
Gwamnan jihar Kwara a Najeriya, Abdulrahman Abdulrazak. Hoto: Kwara State Government.
Source: UGC

Zargin da mabiya addinin gargajiya ke yi

Ajile ta zargi kungiyar da Alhaji Yisa da wani Bureimo Eesu ke jagoranta da yunkurin kai mata hari, bayan sun jefa mata duwatsu da zagi.

Ta ce sun dauki bidiyon lamarin da wayoyinsu suka yada shi a intanet, suna kokarin bata mata suna a idon jama’a.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An yi kutse a shafin gwamnatin Najeriya, an wallafa wata takarda

Ta bayyana cewa ta shafe fiye da shekaru 11 tana zaune a gidanta, tana kuma bin addinin gargajiya tun tana yarinya daga kakarta.

“Ina so in bayyana cewa wannan addini shi ne tushen kakanninmu, shi aka fara amfani da shi wajen kafa Ilorin da sauran garuruwan Yarbawa."

- Yeye Osunfunmilayo Ajile

Ajile ta kara da cewa ibadarta ta kawo tsaro, tana cewa tun na fara ibada, an daina mutuwa a kogi, kuma mutane suna samun amsar addu’a.

Ta ce ta kai rahoto ga Ofishin ‘Yan Sanda A Division a Ilorin, daga nan suka mayar da ita ga kwamitin kare hakkin bil’adama.

Mahaifiyar gargajiyar ta gode wa ‘yan Najeriya da sauran masu gargajiya bisa goyon bayan da suka bata, tana mai cewa ta yi bukukuwanta lafiya shekaru da dama.

Ana rigima tsakanin limamai, mabiya addinin gargajiya

A wani labarin, Kungiyar Limamai a Ogun ta nuna damuwa kan hana zirga-zirga da ake shirin kakabawa a Ikolaje da Idiroko saboda jana’izar Sarki.

Limaman sun ce wannan matakin ya saba wa kundin tsarin mulki da kuma hukuncin kotu da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tun 2017.

Kara karanta wannan

Sabuwar cuta mai cin naman jiki ta bulla a Adamawa, gwamnati ta fara bincike

Sun bukaci Gwamna Dapo Abiodun ya sa baki don hana bikin mabiya gargajiya, da kare rayuka da dukiyoyin jama’a daga barazanar rikici.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com