An ci Gyaran Peter Obi bayan Rashin Mutunta Mai Martaba Sarki a Najeriya
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a LP a zaben 2023, Peter Obi ya fuskanci suka bayan taya sabon Sarkin Ibadan murnar hawa karagar mulki
- Peter Obi ya kira sabon Olubadan, Oba Rashidi Ladoja, “dan uwa”, abin da Reno Omokri ya kira rashin da'a da girmama basaraken
- Omokri ya ce matsayinsa na Olubadan ya wuce kowane mutum, ya gargadi Obi da kada ya yi abin da ba zai yi wa Sarki ba a Arewa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Ibadan, Oyo - Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi ya sake shan suka daga Reno Omokri.
Obi ya fuskanci suka bayan ya kira sabon Sarkin Ibadan, Oba Rashidi Ladoja, a matsayin “dan uwa" yayin taya shi murna.

Source: Twitter
Rashidi Ladoja: Omokri ya dura kan Peter Obi
Reno Omokri, tsohon hadimin shugaban kasa shi ya caccaki Obi a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a jiya Asabar 27 ga watan Satumbar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Omokri ya soki Obi inda ya ce ya kamata tsohon gwamnan ya gane cewa a yanzu Mai Martaba Rashidi Ladoja ba kawai ba ne yana da girma ta sarauta.
A cikin rubutunsa, Omokri ya ce:
“Ladoja ba dan Najeriya kawai ba ne, amma uba ne, bai kamata a kira shi ya kai dan uwa ba.”
“A yanzu, ka ga ne meyasa bai kamata ka kasance mutum nagartacce wanda ya cancanci zama shugaban Najeriya ba?, ba ka hadu ba.
“Abin da kawai ka ke mutuntawa shi ne kudi, kai dan kasuwa ne ba shugaba ba, mutum kamar ka ya fi dace wa ya kasance a yana da shago a kasuwar Onitsha."

Source: Facebook
Martanin yan Najeriya kan sukar Peter Obi
Wasu daga cikin ‘yan Najeriya sun mayar da martani, wasu sun kare Obi, suna cewa Tinubu da Atiku suma sun kira Olubadan “kaninsu.”
Mafi yawa daga ciki sun soki Omokri da cewa hakan ba wani abu ba ne musamman idan akwai alaka mai karfi tsakaninsu.
Abbey Odeyemi ya ce:
“Ba kamar Obi ba, shugaban kasa da Sarki Ladoja suna da kyakkyawar alaka fiye da shekaru 30, hakan na kare bambancin da ake magana."
Mafo ya kara da cewa:
“Ko da Olubadan dan shekaru 20 ne, bai kamata a kira shi da matsayin 'kani ba' hakan rashin mutuntawa ne."
Peter Junior:
"Kullum shi Peter Obi mai zunubi ne amma Tinubu bai yin laifi."
Sabon Sarki ya roki Tinubu kan kirkirar jiha
A baya, mun ba ku labarin cewa Sarkin Ibadan da aka nada ranar Juma'a 26 ga watan Satumbar 2025, Rashidi Ladoja ya roki Bola Tinubu ya raba jihar Oyo zuwa jihohi biyu kafin zaben 2027.
Olubadan na 44 ya yi wannan roko ne a wurin bikin nadinsa da Shugaba Bola Tinubu da wasu manyan kasar nan suka halarta domin shaida wannan gagarumin biki.
Majalisar Tarayya na ci gaba da aikin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya, lamarin da ya jawo kiraye-kirayen kara jihohi domin kara kusanto al'umma da gwamnati.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

