'Yan Sanda Sun Cafke Masu Hada Baki da 'Yan Bindiga Dauke da Kayan Laifi a Katsina

'Yan Sanda Sun Cafke Masu Hada Baki da 'Yan Bindiga Dauke da Kayan Laifi a Katsina

  • Dubun wasu masu hada baki da 'yan bindiga ta cika a jihar Katsina bayan jami'an rundunar 'yan sanda sun yi caraf da su
  • An dai cafke miyagun ne dauke da man fetur wanda su ke shirin kai wa 'yan bindigan da ke ta'addanci kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
  • Majiyoyi sun bayyana cewa an mika mutanen zuwa inda ya dace domin ci gaba da tatsar bayanai daga wajensu a binciken da ake yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama mutane biyu da ake zargi da haɗa baki da ‘yan bindiga.

Rundunar 'yan sandan ta cafke mutanen ne dauke da jarkokin man fetur da su ke shirin kai wa ga 'yan bindiga.

'Yan sanda sun kama masu hada baki da 'yan bindiga a Katsina
Sufeton 'Yan Sandan Najeriya a ofis Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Abin ya yi muni: An bayyana sunayen malami da mutum 4 da suka 'mutu' lokaci Guda a masallaci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sanda sun kama wasu mutane a Katsina

'Yan sanda sun cafke mutanen ne dauke da jarkoki 22 da galan uku na man fetur da ake zargin za su kai wa miyagun mutane a kan iyakar Najeriya da Nijar.

Mutanen da aka kama sun haɗa da Mamuda Umar, mai shekara 50 daga Jibia, da Lawal Hamisu, mai shekara 55 daga Dan Abdullahi a Jamhuriyar Nijar.

Jami'an tsaro masu sintiri a bakin iyaka ne su ka cafke su da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Alhamis a kan hanyar Jibia–Dan Abdullahi.

A cewar majiyoyi, wadanda ake zargin suna cikin wata mota kirar Passat mai launin kore, dauke da man fetur lokacin da aka tare su bayan samun sahihan bayanan sirri.

"An yi zargin cewa man da suke ɗauke da shi an tanadar da shi ne don kai wa ‘yan bindigan da ke addabar al’ummomi a yankunan iyakar Najeriya da Nijar."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka dan sanda, an yi awon gaba da jami'an tsaro

"Hakazalika an mika waɗanda ake zargi da kayayyakin ga sashen binciken manyan laifuffuka (SCID), na 'yan sandan Katsina, domin gudanar da cikakken bincike."

- Wata majiya

Hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa za su ci gaba da sintiri tare da sanya ido, domin rufe dukkan hanyoyin samar da kayan aiki ga kungiyoyin ta’addanci a jihar.

'Yan sanda sun cafke masu laifi a Katsina
Taswirar jihar Katsina, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wani mazaunin Katsina, Shafiu Halliru, ya shaidawa Legit Hausa jami'an tsaron sun yi abin a yaba.

"Sun yi kokari sosai wajen cafke miyagun, muna fatan Allah ya ci gaba da tona musu asiri gabadaya."
"Mutanen nan sun ki bari a zauna lafiya, Allah ya yi mana maganinsu."

- Shafiu Halliru

Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga

Sojoji sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun samu nasarar dakile wani harin 'yan bindiga a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara, an yi awon gaba da mutane masu yawa

Dakarun sojojin tare da hadin gwiwar 'yan sanda da jami'an rundunar C-Watch sun dakile harin ne a wasu kauyuka guda biyu na karamar hukumar Kusada.

Jami'an tsaron sun yi musayar wuta da 'yan bindigan wanda hakan ya tilasta musu tserewa domin tsira da rayukansu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng