Hukumar NAHCON Ta Rage Kudin Aikin Hajji na 2026 a Najeriya
- Hukumar hajji ta NAHCON ta sanar da rage kudin aikin Hajji na 2026 daga N8.5m zuwa tsakanin N8.1m da N8.2m
- Masu zuwa Hajji daga Maiduguri da Yola za su biya N8,118,333.67, sauran jihohin Arewa kuwa za su biya N8,244,813.67
- Hukumar ta yi kira ga maniyyata da su kammala biyan kuɗi kafin 31 ga Disamba 2025 yayin sanar da ragin da aka yi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa (NAHCON) ta sanar da sabon farashin kuɗin aikin Hajji na shekarar 2026.
A sanarwar da ta fitar, ta ce an rage farashin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki tare da amincewar gwamnatin tarayya.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa a watan da ya gabata, NAHCON ta sanar da N8.5m a matsayin kudin wucin gadi na aikin Hajjin bana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai bayan kammala lissafi da tattaunawa, hukumar ta tabbatar da sabon tsari da ya kawo sauƙi ga maniyyata.
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana cewa wannan sauki zai ba da damar samun ibada ga al’ummar Musulmi da dama.
An rage kudin aiki hajjin 2026
A cewar sanarwar hukumar, maniyyata daga yankin Maiduguri–Yola wanda ya haɗa da jihohin Yobe, Borno, Adamawa da Taraba za su biya N8,118,333.67.
Sauran jihohin Arewa kuma za su biya N8,244,813.67. Wannan ya kawo raguwar sama da N200,000 a kan abin da aka karba a shekarar da ta gabata.
Hukumar ta yi bayanin cewa ragin kudin ya fito ne bayan tattaunawa da shugabannin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki.
NAHCON ta yi taro a Saudiyya
Farfesa Abdullahi Sale Usman ya jagoranci tawagar NAHCON zuwa Saudiyya domin kulla yarjejeniya da kamfanonin da za su kula da maniyyata.
An rattaba hannu da kamfanin Mashareeq Al-Zahabiyya da kuma kamfanin sufuri na Daleel Al-Ma’aleem.
A wajen taron, Farfesa Abdullahi ya yaba da irin kulawar da aka bai wa maniyyatan Najeriya a shekarar da ta gabata.
NAHCON ta wallafa a X cewa ya kuma bukaci karin ingantaccen aiki domin tabbatar da kwanciyar hankali da jin dadin mahajjata a shekarar 2026.

Source: Facebook
Shawarwari ga maniyyatan Najeriya
NAHCON ta shawarci dukkan maniyyatan da ke son zuwa aikin Hajjin bana da su tabbatar sun kammala biyan kuɗinsu kafin ranar 31 ga Disamba 2025.
Ta ce hakan zai ba da damar tsara al’amura cikin lokaci tare da tabbatar da cewa an shirya dukkan abin da ake bukata.
NAHCON ta samawa alhazai sauki
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban hukumar alhazai ta kasa NAHCON, Farfesa Abdullahi Sale Usman ya yi bayani kan aikin hajjin 2025.
Malamin ya bayyana cewa an sama wa mahajjata sauki duk da an samu karin kudi a lokacin da aka fara shirin aikin hajjin.
Ya bayyana cewa za su yi iya kokarinsu wajen saukaka aikin hajjin da 'yan Najeriya za su gudanar a shekarar 2026.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

