Abin Ya Yi Muni: An Bayyana Sunayen Malami da Mutum 4 da Suka 'Mutu' Lokaci Guda a Masallaci

Abin Ya Yi Muni: An Bayyana Sunayen Malami da Mutum 4 da Suka 'Mutu' Lokaci Guda a Masallaci

  • Rundunar yan sanda ta bayyana sunayen mutanen da yan bindiga suka kashe a cikin masallaci a kauyen Yandoton Daji a Zamfara
  • Maharan sun aikata wannan danyen aiki ne yayin da ake tsakiyar sallar asubah da safiyar ranar Juma'a a kauyen da ke yankin Tsafe
  • Kwamishinan 'yan sandan Zamfara ya ce yan bindiga sun fara daukar salon kai hari wurin ibada ne domin jan hankalin jama'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara ta tabbatar da harin da wasu 'yan bindiga suka kai masallaci ana tsakiyar sallar Asubah.

Rundunar ta kuma bayyana sunayen wadanda maharan suka kashe da wadanda suka yi garkuwa da su, ciki har da malami wanda shi ne limamin masallacin.

Sufetan Yan sanda na kasa.
Hoton Sufeta Janar na Rundunar Yan Sandan Najeriya, IGP Kayode Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, CP Ibrahim Maikaba, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, in ji Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wuta a masallaci ranar Juma'a, mutane da dama sun mutu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya sa 'yan bindiga suka kai harin

Ya ce yan ta'addan sun kai wannan mummunan hari ne a lokacin da mutane ke tsakiyar sallar asuba da safiyar jiya Juma'a, 26 ga watan Satumba, 2025.

Vanguard ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a masallacin kauyen Yandoton Daji da ke karamar hukumar Tsafe, daya daga cikin wuraren da ake fama da 'yan bindiga a Zamfara.

CP Maikaba ya ce ‘yan bindigar sun yanke shawarar rika kai hari wuraren ibada ne domin jawo hankalin jama’a.

“Mun yi imani cewa ‘yan bindigar sun ɗauki wannan salo ne kawai domin jan hankalin jama’a.
"Sun ga irin martanin da jama’a suka nuna lokacin da aka kai hari wani masallaci a karamar hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina, shi ya sa suka maimaita hakan a nan Zamfara,” in ji shi.

'Yan sanda sun tabbatar da kashe mutum 5

Da yake bayanin yadda lamarin ya faru, kwamishinan yan sanda ya ce yan bindigar sun kashe limamin masallacin da wasu mutum hudu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka dan sanda, an yi awon gaba da jami'an tsaro

“Sun kutsa cikin masallacin lokacin da ake sallar asuba, suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi, suka kashe limamin masallacin tare da wasu mutane huɗu.
“Haka kuma sun sace mutane uku, suka tafi da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.
“Daga baya, bincike ya tabbatar cewa jagoran ‘yan bindiga, Bakin Malam tare da mabiyansa na yankin Makera ne suka shirya wannan hari.”

- CP Ibrahim Maikaba.

Sunayen wadanda aka kashe a Masallaci

Maikaba ya bayyana sunayen waɗanda aka kashe a harin kamar haka:

1. Sale Dangero, mai shekaru 75

2. Mamman Yaro, Mai shekaru 72

3. Malam Lawali Bataribas, 67

4. Malam Jafaru, tsohon ASP na yan sanda

5. Malam Safiyanu, mai shekara 55.

Ya kuma bayyana sunayen waɗanda aka yi garkuwa da su da Danyaye Alhaji Gambo, Malam Basiru, da Ibrahim Bello.

Jami'an yan sanda.
Hoton dakarun 'yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Getty Images

Yan bindiga sun kwashi mutum 40 a masallaci

A wani labarin, kun ji cewa yan bindiga sun sace kusan mutane 40 daga wani masallaci da ke cikin kauyen Gidan Turbe na karamar hukumar Tsafe, jihar Zamfara

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara, an yi awon gaba da mutane masu yawa

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun kewaye masallacin kafin daga bisani su yi awon gaba da mutane.

Rahotanni sun ce iyalan wadanda aka sace sun shiga cikin tashin hankali, yayin da suka yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su dauki matakan gaggawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262