Shugaba Tinubu Ya Hadu da Kwankwaso Gaba da Gaba, An ga Abin da Ya Faru a Bidiyo
- A yau Juma'a, 26 ga watan Satumba, 2025 aka gudanar da bikin nadin sabon Sarkin Ibadan, Oba Rashidi Ladoja a dakin taro na Mapo Hall
- Manyan baki ciki har da Mai Girma Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu da jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabi'u Kwankwaso sun halarci bikin
- Kwankwaso, wanda ake rade-radin zai sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, ya hadu da Bola Tinubu a wurin kuma sun gaisa cikin fara'a
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ibadan, jihar Oyo - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya hadu da manyan jiga-jigan 'yan siyasa na jam'iyyu daban-daban a bikin nadin Olubadan na 44 a jihar Oyo.
Daya daga cikin wadanda Tinubu ya hadu da su kuma suka gaisa akwai tsohon dan takarar shugaban kasa kuma jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Rabi'u Musa Kwankwaso.

Source: Facebook
Mai taimaka wa shugaban kasa na musamman kan harkokin kafafen sada zumunta, Dada Olusegun ne ya tabbatar da hakan a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya gaisa da Kwankwaso a Ibadan
A bidiyon, an ga lokacin da Kwankwaso ya karasa wurin da Shugaba Tinubu yake tsaye kuma ya mika masa hannu suka gaisa tare da musayar kalaman gaisuwa.
Dada Olusegun ya ce:
"Mai Girma Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gaisa da tsofaffin gwamnoni, Olagunsoye Oyinlola, Rabiu Kwankwaso da Ibikunle Amosun (a wurin bikin nadin Olubadan na 44)."
Ana rade-radin Kwankwaso zai shiga APC
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin Kwankwaso ya shirya sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulkin Najeriya.
Lamarin dai ya ja hankalin 'yan siyasa musamman a jihar Kano, inda Kwankwaso ke da tarin magoya baya da kuma 'yan adawa.
A kwanakin baya, Kwankwaso ya fito da kansa ya ce zai iya komawa APC amma bisa sharudda, ba haka nan zai kama ya koma jam'iyyar ba.
A cewarsa, ko da zai koma APC sai an zauna an fada masa yadda za a yi da mutanensa na NNPP da za su biyo shi a dukkan sassan Najeriya.
Wannan ya kara rura wutar jita-jitar cewa tsohon gwamnan na iya komawa APC kowa ne lokaci, musamman da wani labari ya fara yawo cewa ya fara tattaunawa da shugaban jam'iyyar, Farfesa Nentawe Yilwatda.

Source: Facebook
Kwankwaso ya musanta tattaunawa da APC
Sai dai Kwankwaso ya fito ya karyata wannan labari a shafinsa na Facebook, yana mai tabbatar da cewa babu wata jam'iyya da ya cimma yarjejeniyar shiga a yanzu.
Ana cikin haka ne, Shugaba Tinubu wanda shi ne jagoran APC ya hadu da Kwanwkaso, kuma fadar shugaban kasa ta wallafa bidiyon gaisawar da jagororin biyu suka yi a Ibadan.
NNPP ta yi bayani kan shirin Kwankwaso
A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar NNPP, ta musanta jita-jitar da ake yadawa cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yanke shawarar shiga APC.
Shugaban NNPP na kasa, Ajuji Ahmed, ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2023, ba zai sauya sheka zuwa APC mai mulki ba.
A baya dai Kwankwaso ya bayyana cewa jam’iyyarsa a buɗe take ga shiga jam’iyyar APC, amma sai an zaune a tattake wuri.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


