Malaman Musulunci Sun Nemi Kafa Dokar Batancin Annabi SAW a Kano

Malaman Musulunci Sun Nemi Kafa Dokar Batancin Annabi SAW a Kano

  • Kwamitin malaman Sunnah ya shigar da korafi game da kalaman Sheikh Lawal Triumph a ofishin Sakataren Gwamnatin Kano
  • Hakan na zuwa ne bayan an zargi Sheikh Lawal Triumph da yin wasu maganganu da aka ce sun saba da karantarwar addini
  • Yayin da ya ke jawabi, sakataren Gwamnatin jihar Kano ya ce za a yi adalci kuma a guji siyasa wajen daukar mataki kan lamarin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano — Kwamitin malaman masu da’awar Sunnah a jihar Kano sun nemi gwamnatin jihar da ta kafa doka ko ka’ida kan ikirarin zargin batanci ko zagin Annabi (SAW).

Sheikh Abdallah Gadon Kaya ne ya bayyana hakan yayin ganawa da sakataren gwamnatin Kano a jiya Juma'a.

Sheikh Gadon Kaya da sakataren gwamnatin Kano
Sheikh Gadon Kaya da sakataren gwamnatin Kano. Hoto: Karatuttukan Malaman Musulunci
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka yi zaman ne a cikin wani bidiyo da Awaisu Al-Arabi Fagge ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Kazamin rikicin manoma ya firgita Darazo, ya hana zuwa gona a Bauchi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bukatar kafa dokar batanci a jihar Kano

A ganawar malaman da Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, Sheikh Abdallah Gadon Kaya ya yi godiya ga gwamnati da ta ba su damar gabatar da korafi a rubuce.

Ya jaddada cewa malamai ne suka dace su tabbatar da ko wani abu ya kai ga batanci ko akasin haka kafin a dauki mataki.

Gadon Kaya ya ce an samu tashin hankali tsakanin wasu bangarorin addini a baya, lamarin da ke bukatar a samu doka da za ta hana tashin hankali a kafafen sada zumunta da wuraren taro.

Malamin ya ce ya kamata a saka dokar hana cewa wani ya yi batanci wa Annabi (SAW) a kafafen sadarwa ko a cikin gari har sai majalisar shura ta tabbatar da abin da aka fada batanci ne.

Wasu daga cikin malaman da aka zauna da su
Wasu daga cikin malaman da aka zauna da su. Hoto: Karatuttukan Malaman Musulunci
Source: Facebook

Ya ce idan aka kyale kowa ya rika cewa an yi batanci wasu za su iya amfani da sabanin da ke tsakaninsu da mutane su ce sun yi batanci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano za ta dauki mataki kan malamin da ake zargi da taba mutuncin Manzon Allah SAW

Karin bukatun malaman ga gwamnati

Sheikh Kabir Abdulhamid ya nemi gwamnati ta dauki mataki idan an yi wa malamansu kazafi kan batanci.

Barista Ishaq Adam Ishaq ya bayyana cewa zai iya yiwuwa abin da ya faru na korafin na da alaƙa da sabanin siyasa tsakanin Malam Triumph da gwamna Abba Kabir Yusuf.

A kan haka ya bukaci gwamnatin Kano da ta lura da kyau ga masu neman amfani da banbancin siyasa a rikicin addini.

Malam Triumph da aka shigar da korafi a kansa
Malam Triumph da aka shigar da korafi a kansa. Hoto: Sheikh Lawal Abubakar Shuaibu Triumph
Source: Facebook

Martanin gwamnatin Kano ga malamai

Sakataren Gwamnatin Kano, Umar Farouk Ibrahim, ya ce an karbi dukkan korafe-korafen a rubuce.

Ya kara da cewa gwamna Abba Kabir Yusuf bai ɗauki lamarin a matsayin na siyasa ba, kuma gwamnati za ta tabbatar an yi wa kowa adalci.

Legit ta tattauna da Muhammad Sani

Wani malami mai suna Muhammad Sani ya bayyana wa Legit cewa yana goyon bayan kafa dokar batanci a Kano.

Muhammad Sani ya ce:

"Yana da kyau a samar da irin dokar domin kare rayukan al'umma da kuma hana tashin hankali.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace basarake tare da wasu mata a Plateau

"Da zarar an samu wani da ba shi da ilimi ya yi zargi, za a iya kashe mutum ba tare da bincike ba."

An mika korafi kan Triumph ga shura

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano ta tabbatar da karbar korafe korafe game da Sheikh Abubakar Triumph ga majalisar shura.

Sakataren gwamnatin jihar ya tabbatar da cewa kungiyoyi takwas ne suka shigar da korafi game da zargin da ake yi.

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta tabbatar da cewa za a yi wa kowa adalci wajen hukuncin da za a yanke bayan shawarar da kwamitin shura ya bayar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng