Nadin Sarauta: Sarkin Musulmi Ya Isa Ibadan, ana Dakon Tinubu da Atiku
- Yayin da ake jiran Bola Tinubu, wasu gwamnoni sun isa Ibadan domin halartar bikin nadin Oba Rashidi Ladoja a matsayin sabon Olubadan
- Ana sa ran taron ya samu halartar manyan baki ciki har da Shugaban kasa, Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso, da wasu sarakunan gargajiya
- Sarkin Musulmi ya isa jihar yayin da gwamna Seyi Makinde ya dakatar da hutunsa don halartar bikin tare da yin biyayya ga al’adun jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Oyo - A yau, garin Ibadan na jihar Oyo ya kafa tarihi yayin da aka kaddamar da nadin Oba Rashidi Adewolu Ladoja a matsayin Olubadan na 44.
Rahotanni sun nuna cewa babban bikin yana gudana ne a dakin taron Mapo, inda aka tara manyan baki daga fadin Najeriya.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa bikin nadin Ladoja ya kasance abin alfahari ga mutanen Ibadan da yankin Yarabawa baki daya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bakin da za su je nadin sarautar
Ana sa ran shugaba Bola Tinubu ya halarci taron tare da gwamnoni daga sassa daban-daban, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar.
Kwamitin taron ya bayyana cewa ana tsammanin tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso wajen nadin sarautar.
Hakazalika, ministoci, ’yan majalisa da fitattun mutane daga fannoni daban-daban za su hallara wajen.

Source: Facebook
Sarkin Musulmi ya isa garin Ibadan
Manyan Sarakunan irin su Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, Alaafin na Oyo sun hallara.
Haka zalika Oba Akeem Owoade, da sauran manyan sarakuna kamar Soun na Ogbomosho da Oluwo na Iwo sun isa domin karrama sabon Olubadan.
Maganar kwamitin nadin sarautar
Shugaban kwamitin bikin nadin, Bayo Oyero, ya bayyana cewa nadin sarautar alama ce ta tarihi da kuma tabbatar da tsarin mulkin gargajiya a kasar Ibadan.
Ya ce shigowar Oba Ladoja kan karagar mulki wani tafarki ne da aka gina tun shekaru da dama, tare da bin tsarin da iyaye da kakanni suka shimfida.
Oyero ya kara da cewa kasancewar Ladoja tsohon Sanata kuma tsohon gwamna zai samu damar fahimtar al’umma da kuma jagorantar al’ummarsa cikin basira.
Gwamna Makinde ya dawo daga hutu
Daily Trust ta wallafa cewa gwamna Seyi Makinde ya katse hutunsa da wuri domin halartar bikin tare da kula da shirye-shirye kai tsaye.
Majalisar dokokin jihar ta amince da dawowarsa daga hutu, inda mambobin suka yaba da wannan mataki a matsayin shaida ta kishin al’adu da martabar jihar.
Makinde ya bayyana cewa wannan biki tarihi ne da bai kamata ya gudana ba tare da kasancewarsa a wajen taron ba, don haka ya zabi dawo wa aiki kafin wa’adin hutun ya kare.
An nemi cire sarki a jihar Osun
A wani rahoton, kun ji cewa mutane sun fara zanga zanga domin neman gwamnan jihar Osun ya tsige Oba Joseph Oloyede.
An nemi tsige Sarkin Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede ne bisa kama shi da laifi dumu dumu da aka yi a kasar Amurka.
Bayan kama Sarkin da laifin karkatar da kudin tallafin Covid-19, wata kotun Amurka ta masa daurin sama da shekara hudu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


