Yadda Ƴan Bindiga ke Koro Mutane a Sakkwato, An Tilasta wa Jama'a Hijira
- Ƴan bindiga sun ƙara kai hari a ƙananan hukumomi daban-daban a Sakkwato, inda suka kashe mutane da dama tare da sace wasu
- Hare-haren sun sa mazauna garuruwa irin su Dinawa, Achida, Saketa, Manuna da Caco cikin halin firgici, kuma an fara gudun hijira
- Mazauna sun bayyana cewa hare-haren sun zama tamkar kasuwanci ga ƴan bindiga, domin kusan kullum sai sun shiga wani gari su yi barna
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto – Mazauna garuruwan Dinawa, Achida, Saketa, Manuna da Caco a ƙaramar hukumar Wurno ta jihar Sakkwato sun bayyana irin mummunan halin da suke ciki.
Wani mazaunin garin Dinawa ya bayyana cewa mahaifinsa na cikin waɗanda 'yan bindiga su ka aka kashe a harin baya-bayan nan yayin da ake ƙara kai hare-haren ta'addanci.

Source: Twitter
BBC Hausa ta wallafa cewa mazauna yankunan suna cikin mummunan tashin hankali, saboda zaman gidajensu ya gare su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mazauna garuruwan Sakkwato sun koka
Wani mazaunin garin Dinawa ya ce ana kashe masu iyaye, mata da yara kuma kusan kullum ana kai masu hari.
Ya ce:
“Muna cikin tashin hankali da ɗimuwa da firgici. Jiya ma sun shiga garin Manuna suka kashe uba da ɗansa da mata guda huɗu. A garinmu kuma na Dinawa, ni kaina sun kashe mun mahaifi.”
Ya ƙara da cewa duk rana sai an kai hari a wani gari, inda lamarin ya zama kamar cin kasuwa, inda su ka dage wajen kai hari akai-akai.

Source: Original
Mazaunin garin ya ce:
“Yanzu kowacce rana ta Allah, idan suka shiga wannan gari yau, gobe sai wani. Sun mayar da abin kamar kasuwanci ne.”
Jama'an Sakkwato na barin garuruwansu
Wasu mazauna jihar Sakkwato sun bayyana cewa da yamma ta yi kowa yana barin gida domin neman mafaka a wasu yankuna kamar Achida, Wurno ko ma garin Sokoto.
Sun bayyana cewa daukar wannan mataki ya zama tilas, saboda babu wanda ke iya kwana a garuruwansu cikin kwanciyar hankali.
Hare-haren sun tilasta wa mutane da dama yin gudun hijira daga gidajensu, wani mazaunin Achida ya bayyana cewa dubunnan mutane ne ke komawa daga garuruwan Caco da Dinawa.
Ya ce:
“Al’umma gasu nan suna ketowa, ka ga har ma wasu manyan motoci suna kwasar daruruwan mutane zuwa kudu. Amma ba kowa ne za a iya karɓa ba saboda matsin tattalin arziki da muke ciki."
Ya ƙara da cewa hanyar Caco yanzu ta zama tamkar Sambisa, domin da zarar ƙarfe biyar na yamma ta yi, babu wanda zai iya bi saboda hatsarin harin ƴan bindiga.
A halin da ake ciki, al’ummomin yankin sun roƙi gwamnati da hukumomin tsaro su kawo masu ɗauki da taimako.
Hatsari ya rutsa da masu tserewa yan bindiga
A baya, mun wallafa cewa rahotanni daga jihar Sakkwato sun tabbatar da aukuwar wani mummunan hatsarin jirgin ruwa a ranar Alhamis, 18 ga watan Satumba, 2025.
Wani jirgin ruwa da ke ɗauke da mata da yara — waɗanda suka fito daga yankin da ‘yan bindiga suka kai hari — ya nutse yayin da yake ƙoƙarin ketare wata gada.
A cewar shaidun gani da ido, hatsarin ya faru ne bayan jirgin ya bugi bakin gada, lamarin da ya haddasa kifewar sa kuma a nan ne jama'a su ka rika kawo agaji domin ceto wasu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


